Wani Tsoho ya mutu ya dawo a Kasar
China
– Wani Dattijo ya mike daga cikin
akwatin kabarin sa yayin da ake masa jana’iza
– Tsohon mai shekara 75 ya mutu ya
dawo
– Wannan abu ya ba Jama’a mamaki
Wani
Tsoho mai shekaru 75 a Duniya ya farka ya samu kan sa a cikin kabari ana shirin
birne sa. Wannan abu dai ya faru ne da wani Dattijo mai suna Huang Mingquan a
Kasar Sin watau Kasar China.
Kamar
yadda Jaridun Kasar China suka rahoto, wannan tsoho yana mikewa sai ya fara
tambayar ‘me ke faruwa a nan?’ ‘Wai birne ni za ku yi…?’ Wannan Tsoho dai ya
samu kan sa a kudundune cikin akwatin katako na gawa tare da ‘Yan uwa da abokan
arziki a zagaye da shi ana jana’iza.
Wannan
Mutumi dai yayi doguwar suma ne watakila, bayan da aka lura ya daina numfashi
sannan kuma jikin sa yayi sanyi, sai aka dauka cewa ya rasu ne. Nan take ‘ya
‘yan sa da jikoki suka fara shirin birne sa.
Sai
dai bayan kusan awanni takwas wannan mutumi ya farka, sai aka gan sa kawai
dame-dame a kan akwatin gawan da ya ke ciki. Wannan abu dai da ya faru a Garin
Junlian na Kasar China ya ba Jama’a mamaki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment