Yau Donald Trump zai canji Barrack Obama a Amurka
Tun daga farkon
tafiyar, Donald Trump ya ba mutane mamaki, babu wanda ya taba tunanin zai tsaya
takara, ina ma kuma ace ya ci tikitin Jam’iyyar Republican, yau kamar wasa Trump zai zama Shugaban Kasar Amurka na 45
a Tarihi. Mutumin da bai taba rike ko cokali a Gwamnati ba, ya zama Shugaban
Kasa, kuma Kasa irin Amurka.
Kuri’un Bakaken fata
Donald Trump
yayi nasara a Garuruwan da kuri’un bakaken fata ke da dama, irin su; Ohio,
Florida, da North Carolina. Wadannan Garuruwa, asalin su tun fil azal Jam’iyyar
Democrat suke yi, wannan karo, Trump
da Jam’iyyar sa, sun yi nasara. Fararen fatar da ke irin wannan Yanki musamman
marasa karatu sun fito kwan su-da-kwarwatar su wajen ganin Trump yayi nasara.
Mutanen Virgina,
Colarado, da Wisconsin sun ba Clinton mamaki da kunya, duk ta cewa ta ci sauran
Yankin da bakaken fata ke da galaba, irin su: Birnin New York da California,
Bakaken da ke Jihar Utah sun kada ta. Dama can wasu musamman ‘Yan karkara suna
ganin Shugaba Obama bai tsinana masu komai ba a shekara 8. Ko daama can Trump
na da goyon bayan sauraren farare.
Trump bare ne
Hillary ba yau
ta saba shiga Gwamnati ba, asali ma Mijin ta ya taba Shugabancin Kasar Amurka.
Ita da kan ta, ta taba neman takara, ta kuma rike Sakatariyar Gwamnati. Don
haka sune manyan Kasar, an dade ana damawa da su, ba yau ta shigo ba. Shi kuwa,
Trump, kasuwancin sa kurum ya sa gaba, bai taba siyasa ba ko shiga cikin Gwamnati.
Wannan ya sa wadanda ba su son zaben mala’u, suka bi shi.
Tun a cikin
Jam’iyyar sa, Trump ya buga da su; Ted Cruz, Ben Carson, Marco Rubio, Jeb Bush
da su Gwamna Kasich, amma duk sun buga sun bar sa. Paul Ryan, wanda yake
Shugaban Majalisar Kasar, ya nuna adawar sa a fili ga Trump, duk da su na
Jam’iyya daya, hakan kuwa ya ma kara masa farin jinni. Kai har su John Mc Cain
sun yi ta da Trump, amma wane mutum?
Trump: Kwangiri, karfen jirgi
Duk yadda za ayi
a kauda Donald Trump an yi, amma Gogon ba ya jin bugu. Ga shi dai an fi sa
kashe kudi wajen Yakin neman zaben, Shugaba Obama da kan sa, ya tashi tsaye
wajen ganin Hillary ta kawo Amurka, amma ina!
Trump ya iya
magana, kamar yadda Sir Elton John ya fada, yana da shegen baki. Ko da yake
cewa wasu lokutan akwai kazanta a maganganun, amma magoya bayan sa, wasu mutanen
Amurka, abin da suke son ji kenan. An zarge sa da laifin lalata da matan mutane,
ga kuma cewa ba ya biyan ma’aikata balle haraji ga Gwamnati, amma duk ya
tsallake wannan. Ya zagi kowa, ya kuma kwana lafiya, har ‘Yan Jam’iyyar sa, ba
su sha ba. Trump yayi rikici da ‘Yan Jarida, mata, Jama’a da dama, dsr, kuma
bai yi nadamar hakan ba, sam!
Zargin da ke kan Misis Clinton
Lokacin da
Hillary Clinton ta ke Gwamnati ta goge Sakonnin Email sama da 30,000 daga
akwatin ta na gida, Trump yayi amfani da wannan laifi ko abin da za a kira sa
wajen doke Clinton. Trump har yayi ma Clinton alkawari zai daure ta saboda
wannan idan ya hau mulki. James Comey na Hukumar Bincike na Amurka ya kara tado
maganar daf da zabe da baki suka yi yawa.
Yayin da Clinton
ke kokarin wanke kan ta, Trump ya shiga wanke tunanin magoya bayan ta. Hakan ya
taimaka masa ainun wajen lashe ko samun kuri’u masu tsoka a inda Clinton ke da
wayau. Trump ya ratsa Garuruwan da ake tunanin sun fi karfin sa a wannan
lokaci, ko da ya gane yadda Sakamakon zaben da aka rika gudunarwa a Gidan
Talabiji suke tafiya. Ba shakka, FBI ta lalatawa Clinton tafiya.
Trump ya fito a mutum
Donald Trump
yayi wani irin yakin neman zaben da ba a taba yin irin sa ba a Tarihi. Trump ya
caccaki wanda ya ga dama, yayi gatse, yayi zage-zage, yayi rikici da dan kowa, kai
har magoyan bayan sa, sai su na hakuri da shi.
Trump bai yi ta
mutane ba, ko yayi amfani da siyasa ko ya rika saka ma bakin sa linzami, A’a, namijin
ba ruwan sa, wasu kuma hakan suke so, ko da basu fito fili ba. Yayin da wasu
irin ‘Yan Boko ke masa kallon mahaukaci, yau ga wannan mahaukaci ya zama
Shugaban Kasa na Amurka.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan daga Anthony Zurcher na BBC
[Na taba buga wannan labarin a baya]
No comments:
Post a Comment