– Dan tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomole ya fito takara
– Dr. Cyril Oshiomole yana neman kujerar Majalisa
– Babban
Dan tsohon Gwamnan yace yanzu lokaci ne na matasa
Dan tsohon Gwamnan Jihar
Edo, Adams Oshiomole ya fito takarar Dan Majalisar Wakilai na Tarayyar Jihar.
Dakta Cyril Oshiomole dai ya kama hanyar Mahaifin na sa wanda yayi shekaru 8 a
matsayin Gwamnan Jihar Edo.
Dakta Cyril Oshiomole yace
yanzu fa lokaci ne na samari ba tsofaffi ba. Babban Dan tsohon Gwamnan dai yana
neman kujerar Mazabar Etsako a Majalisar Tarayya. Tsohon Dan Majalisar Yankin,
Philip Shu’aibu ya dai zama Mataimakin Gwamnan Jihar.
Yanzu haka fastoci sun shiga
Garuruwa irin su Auchi, Benin, Etsako da sauran su. Dakta Oshiomole dai ya fito
ne a karkashin Jam’iyyar APC. Ana dai tunani Shugaba Buhari zai nada Adams
Oshiomole wani matsayi bayan da aka gan su tare kwanaki a cikin Villa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment