Thursday, January 5, 2017

An harbe wata mata a Aso Rock



An harbi wata mata a Fadar Shugaban Kasa da kuskure


Wani Jami’in DSS ne ya saki linzamin bindigar sa bai sani ba


Yanzu haka an yi Asibitin Villa da ita




A jiya an samu tuntube a Fadar Shugaban Kasa inda aka narkawa wata mata dalma ba da gan-gan ba. Yanzu dai an kai wannan mata ma’aikaciyar Gidan Gwamnatin zuwa Asibiti domin samun lafiya.

Wannan tsautsayi ya faru ne Jiya Laraba bayan da wani Jami’in Hukumar DSS ya saki bakin linzamin bindigar sa bai sani ba. Jami’in yana kokarin ajiye bindigar sa a Kasa kenan kawai sai ya saki harsahi a cikin wannan mata.

Wanda abin ya faru a gaban idon sa yace an yi wa wannan mata rauni a ciki da cinya da dalma. Yanzu haka dai tana Asibitin Gidan Gwamnatin da ke Fadar Shugaban Kasa inda ake kula da raunin.

Idan ba a manta ba dai kasafin kudin bana na sama da Naira Tiriliyan 7, Fadar Shugaban Kasa za ta kashe sama da makudan kudi wajen sayen cokula cin abinci. Wasu dai na ganin ana facakali da kudin al’umma a Kasar



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...