– Sanatocin APC sun tsige Ali Ndume daga Shugaban masu rinjaye a Majalisar
– Sanatoci 39 na APC cikin 63 suka
sa hannu wajen tunbuke Ndume
Sanatoci
39 cikin 63 na Jam’iyyar APC da ake da su a Majalisar Dattawa suka saka hannu
wajen tsige Ali Ndume daga kujerar sa. Tuni kuwa dai har an nada Sanata Ahmed
Lawan a matsayin wanda zai maye gurbin na sa.
A
wani kudirin da ke nuna rashin amanna da Sanata Ndume, Shugaban Majalisar
Dattawar, Bukola Saraki, ya karanta takardar da ‘Ya yan APC suka aiko na cewa
sun cire Ndume. Sai dai tuni ya wanke kan sa, yace ba shi ya kashe zomon ba,
rataya kurum aka ba shi.
Sanatocin
da suka cire Ndume dai sun hada da: Dino Melaye, Sulaiman Nazif, Mustafa Bukar,
Barau Jibrin, Rabiu Kwankwaso, Usman Nafada, Baba Garbai, Kabir Marafa,Tijjani
Kaura, Sulaiman Hunkunyi, Shehu Sani, Ubale Shitu, Aliyu Abdullahi, Umaru
Kurfi, Abubakar Yusuf, Kabir Gaya, Shaba Lafiagi, Ibrahim Gobir, Isa Misau.
Saura
sun hada da Ali Wakili, Ahmed Bakura, Ahmed Lawan, David Ummaru, Danjuma Goje,
Binta Masi Garba dsr. Shi dai Sanata Ahmed Lawan yace ba don yana son kujerar sai hau ba.
No comments:
Post a Comment