– Sarkin
Jama’a ya tsallake rijiya da baya bayan an kai masa hari
– Fulani
Makiyaya suka kai ma Sarkin hari
– Allah
yayi da sauran kwanan Sarkin na Kafanchan
A jiya ne Sarkin Kafanchan
ya tsallake rijiya da baya bayan da Fulani Makiyaya suka kawo masa hari. Saura
kiris dai maharan su ga bayan Sarkin Jama’an. Allah dai ya tsaga da rabon
kwanan mai martaba a gaba.
Duk da dai Sarkin ya tsira
da kyar, Maharan sun yi kaca-kaca da motocin da ke tawagar sa. An dai dagargaza
motoci uku da ke takewa Mai martaba Sarkin baya a harin da aka kai. Maharan dai
sun tare Sarkin ne yayi da yake dawowa daga Garin na Kafanchan.
Idan ba a manta ba Sarkin da
sauran takwarorin sa na Jihar, sun gana game da batun tsaron Yankin da Mai
girma Gwamna Malam Naisru El-Rufa’i a Garin Kaduna. Tuni dai dama Gwamnan ya
kafa dokar hana fita a Yankin. Shi ma dai Ciroman Jama’a, Alhaji Kabiru Tanko da
kyar ya sha.
Dama dai jiya wani Dan
Majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Kaura da ke cikin Yankin Kudancin
Kaduna, Honarabul Gideon Gwani ya koka da yadda lamarin tsaro ya tabarbare a
Yankin. Dan Majalisar yace Mutanen suna cikin matsala don kullum cikin kai masu
hari ake.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment