– Shugaba Buhari ya rubuta takarda ga Majalisa cewa zai tafi hutu
–
Mataimakin sa, Osinbajo zai karbi ragamar Kasar
– Shugaba
Buhari zai yi tafiya na kwanaki 10
Rahotanni da ke zuwa mana suna nuna cewa Shugaba
Buhari zai tafi hutun kwanaki 10. shugaban majalisar dattawar Kasar Bukola
Saraki ya karanto takardar shugaban kasar da ke neman izini.
Shugaba Buhari ya nemi Majalisa ta amince da
Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasar.
Wannan dai yana cikin kundin tsarin mulkin kasar sashe na 145 bangare na I.
Kuma ba dai wannan bane karo na farko da shugaban
kasar Muhammadu Buhari ya tafi hutu, aka mika shugabancin kasar hannun Yemi
Osinbajo ba. A watan Fabrairun bara da kuma Yunin shekarar yayi hakan. Shugaba
Buhari ya bayyana a shafin san a Facebook cewa zai tafi hutu Kasar Ingila na
kwanaki 10.
A jiya ne Abba Kyari ya isa Garin Maiduguri tare da
sauran tawagar shugaban kasar da ya jagoranta domin jaje ga mutanen Borno. Sauran
tawagar sun hada da Shugabannin Hafsun Sojojin Kasar da kuma Ministocin tsaro
da na yada labarai.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment