– Najeriya ta koma ta 1 ta a jerin masu hako man fetur
–
Kasar Najeriya ta doke Angola a Afrika
– Najeriya
ta fita daga wannan matsayin tun a bara
Najeriya ta komo matsayin ta
na farko a jerin Kasashen da ke hako man fetur a Nahiyar Afrika. Najeriya dai
ta doke Kasar Angola bayan Kasar ta dauki watanni kusan 7 suna matsayin na
farko a Nahiyar gaba daya.
A bara ta kai Angola tana
hako da gangar mai miliyan 1.7 yayin da Najeriya ba ta hako abin da ya wuce
1.5. Wannan dai zai bayu ne ga matsalolin da aka rika samu daga Tsagerun
Neja-Delta. A watan Disamban da ta wuce ne dai harsashen Kungiyar OPEC ya nuna
cewa Najeriya ta kerewa Kasar Angola da kusan ganga 100,000.
Kungiyar OPEC ta bayyana
cewa Najeriya ta zarce Angola bayan yarjejeniyar da aka yi na rage yawan man da
ake hakowa a kowace Kasa. Wannan zai sa Kasar Angola da rage ganga 78,000 a
kowace rana.
Kungiyar OPEC ta Kasashen
Duniya masu fitar da man fetur ta bayyana Dan Najeriyar nan, Mohammed Barkindo
a matsayin Gwarzon wannan shekarar. Mohammed Barkindo wanda shine Sakataren
Kungiyar yayi namijin kokari wajen tashin farashin gangar mai a Duniya daga Dala
$30 zuwa sama da Dala $50 a kasuwannin Duniya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment