– Ofishin
Mataimakin shugaban kasa ya karyata rade-radin cewa ana nema a tursasa Osinbajo
yayi murabus
– Mai
ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa yayi bayani
– Sanata
Ojudu yace wannan karyar banza ce
Ana ta yada rade-radin cewa
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na shirin ajiye aiki bayan
matsin lamba da yake samu. Fadar Shugaban Kasa dai ta yi wuf ta maida martani
ga masu yada jita-jitar inda tace sam karyar banza ce ba gaskiya ba.
Mai ba Shugaban kasa shawara
a game da harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu yayi jawabi daga Fadar
Shugaban kasar. Sanata Ojudu ya bayyanawa Jaridar Punch cewa rade-radun da ke
yawo ba gaskiya bane. Rahotanni sun bayyana a baya cewa wasu Gwamnoni na neman
tursasa Osinbajo yayi murabus.
Sanata Ojudu yace babu
kanshin gaskiya ko na sisin kwabo a cikin maganar. Yanzu haka dai Mataimakin
Shugaban kasar ne ke rike da Kasar a matsayin mukaddashi. Kuma yana kan aiki ba
dare ba rana.
No comments:
Post a Comment