– Sojojin Najeriya sun ce ba su san
inda Abubakar Shekau yake ba
– Wani Kwamandan Sojin yake cewa
maganar ace Shekau na Kala-Balge duk rade-radi ne
– Sojojin Kasar dai sun share
Dajin Sambisa, sun ce Boko Haram kuma har abada
Rundunar
Sojin Najeriya ta bayyana cewa ba ta san inda Shugaban Kungiyar Boko Haram din,
Abubakar Shekau ya shige ba. Rundunar Sojin Kasar suka ce maganar cewa Shekau
din ya tsere zuwa Kala-Balge ko wani wuri can duk rade-radi ne wanda ba wanda
zai iya tabbatarwa.
Manjo
Janar Irabor Lucky wand shine Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole yace sun rasa gane inda Shekau din ya shige.
Kwamandan yace da zai gan sa, da ya kuwa damke sa. Kwamandan dai ya kara
tabbatar da cewa an gama da Boko Haram a Yankin.
Sojojin
Kasar dai sun kira Jama’a su bada na su gudumuwar domin samun zaman lafiya a
Yankin Kasar. Ana dai cigaba da kama ‘Yan Boko Haram da dama a cikin Kasar, sai
dai har yanzu babu labarin Shekau.
Mai
taimakawa shugaban kasar, Muhammadu Buhari wajen yada labarai Mista Femi
Adesina, yace Yakin Boko Haram ba na taho-mu-gwabza bane, hakan ya hana a kama
Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau tuni.
No comments:
Post a Comment