– An
kama wani Dan Najeriya da laifin kisa da fyade a Ingila
– Tuni aka yanke masa hukuncin dauri
– Dan
Najeriyar dai dan manya ne a can ya kuma zo karatu ne
An samu wani Dan Najeriya da
laifin fyade da kuma kashe wata mata a can Kasar Scotland. An dai kama wannan
yaro ne da laifin yi wa wata mata mai-zaaman ka ta fyade, daga karshe kuma ya
kashe ta.
Wannan yaro dai ya aikata
wannan mummunan laifi ne jim kadan bayan zuwan sa Kasar domin karatu a Jami’ar
Robert Gordon ta Birnin Abardeen. Mahaifin sa dai wakilin Najeriya ne a Kasar
ta Scotland.
Bala Chinda mai shekau 26
dai yayi lalata da Jesica McGraa kafin ya kashe ta a shekarar bara ta 2016. Duk
da ya karyata hakan, bincike ta na’urar daukar hoto na CCTV sun nuna cewa Bala
ya ja Marigayiya Jesica zuwa dakin kwanan sa, wanda daga nan ba a kara ganin ta
ba, sai gawar ta.
Kotu dai ta yankewa Bala
Chinda hukucin daurin rai-da-rai bayan an gano cewa ya kashe wannan mata mai
zaman kan ta. Watakila dai shake ta aka yi har ta mutu, ana kuma tunanin
rikicin kudi ne ya hadu su.
Allah ya tsare.. Ameen
ReplyDeleteAmin kam
ReplyDelete