Saturday, December 31, 2016

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA




'Dagewa wajen neman abin dogaro da kai'-Daga Bakin Imam Dr. Mustapha Isa Qasim


A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman Ar-Raheem,
‘Yan uwa Musulmi, Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah wa Barakatuh,
Muna masu godiya ga Allah Madaukakin Sarki godiya da ya kawo mu wannan Rana ta Jumu’a. Allah ya sa mu dace da sa’ar da ake gafarta zunubi a wannan Rana. Amin.
Wannan Huduba tamu tana magana ne a game da neman halaliya watau abin dogaro da kai. Yana da muhimmaci a jawo hankalin ‘Yan uwa a game da wannan batu, domin kuwa shine asasi na rayuwa. Musulunci ya kafa rayuwa a kan neman abin dogoro; aiki, noma, kasuwanci domin kuwa akwai albarka a ciki. Ta haka ne Mutum zai kasance ya samu abin da zai ci tare da Iyalin Sa na Halal.
Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, muna neman taimakon Sa, Muna neman tsari daga munanan ayyukan mu. Duk wanda Allah SWT ya shiryar shi ne shiryayye, wanda kuma Ya batar, babu wanda zai shiryar da shi. Muna neman shiriya daga Allah SWT shi kadai. Muna kuma shaidawa Allah shi kadai yake, babu wani abin bauta da gaskiya face Shi. Sannan Muna yin shaida cewa Annabin Mu, Annabi Muhammadu SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon Sa wanda Allah SWT ya aiko sa da Addini na Gaskiya.
‘Yan uwa wajibi ne mu ji tsoron wajen neman Halal. Musulunci dai Imani ne na gaskiya, sai dai Mutum ba ya zama da Imani ba tare da aiki ba. A duk lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya ambaci cewa ayi Imani, sai an ambaci cewa ayi aiki na gari. Yana daga cikin aiki na gari; neman arziki na halal. Ba a nufin cewa Mutum zai samu aiki mai kyau kawai yayin da Mutum ya je Masallaci ko Aikin Hajji, A’a, Har Mutumin da yake noma, idan har yayi da niyya kyakkyawa tare da bin shari’a, wannan ya zama Ibada. Watau dai Dan kasuwa, Ibada yake yi, Haka Dan Makaranta… Allah ya ambaci Imani da aiki na gari a wurare masu dinbin yawa a cikin Al-Kur’ani.
‘Yan uwa bai halatta ga Musulmi ya zama mai kasala wajen neman arzikin sa ba. Ka da Mutum yace shi ba zai yi wani aiki; kasuwa ko noma dsr ba domin shi ya kebantu da ibada. Kuskure ne haka, ko Mutum yace shi ya dogara da Allah mai girma domin Shi yake badawa. Aya cikin Suratul Jumu’a tana da umarni a fita a nemi arziki cikin Kasa. Haka bai hallata Mutum ya dogara da Sadaka ko kyauta wajen wani ba. Abin da ya dace shine idan Mutum ya cancanci Zakka ko wata Sadaka, sai ya karba, ba ya zama yana jira a kawo masa ba. Bai hallata mutum mai karfi da lafiya ya rika jira a kawo masu sadaka ko wani taimako ba, wannan ba tawakalli bane illa kuskure. Matukar Mutum ya fita neman arziki na Allah, to Ubangiji zai ba sa. Kamar yadda Manzo SAW yake cewa bai halatta a ba Mutum, mai karfi-mikakke Sadaka ba. Sannan kuma idan har Mutum ya rayu a haka zai zama cikin wulakanci da kaskanci har ma suna fada cewa: Allah ya ba ku, mu samu…ka da Mutum ya zama kullum shi ne mai karba, domin kuwa hannun da ke mikawa ya fi alheri a kan hannun da ke karba. Ina laifin ko da kana karba, wata rana ka zama mai badawa? Haka dai kuma akwai wani Hadisi daga Manzon Allah SAW wanda yake cewa: Roko da bara da neman taimako, Mutane ba za su daina wannan ba, har sai sun hadu da Allah SWT a Ranar Lahira, babu wani yanki na tsoka a jikin fuskan su. Naman su duk zai sale, daga an hange su, za a gane cewa sun zama masu bara hannun Mutane a Duniya.
A game da dogaro da kai; Manzon Allah SAW yana cewa: Daya daga cikin ku, ya dauki gatari da igiya ya saro itace a daji, ya dauko a bayan sa, ya saida, ya fi masa alheri a kan ya tambayi Mutane, watakila su ba sa, ko kuma su hana sa. Idan har Mutum ya lura da wannan, yana nuna cewa ya kamata Musulmi mai karfi ya fita ya nema na sa, Idan har Mutum ya fita, lallai kuwa Allah SWT zai ba sa. Allah SWT kuwa yana cewa: Ku nemi arziki a wajen Allah domin shi kadai yake badawa. Duk wanda ka gani da Arziki, to Allah SWT ne ya ba sa, don kuwa ba shi Mutum ne ya ba kan sa ba, kai ma idan ka nema sai ya ba ka. Sai dai kuma ba a nufin cewa Ubangiji zai ba kowa daidai wadaida, wannan rabo ne na Allah mai Girma. Don haka ka da ka ji haushin wani don ya fi ka, Allah SWT zai ba ka gwargwadon abin da kake bukata. Duk wanda aka dai ba, ya zama jarrabawa gare sa; haka wanda bai samu ba, hakuri zai zama jarrabawa gare sa.
Mu sani cewa daga cikin neman abin dogaro da kai akwai abubuwa da dama; kiwo, sana’a, kasuwanci, noma, aiki irin na Gwamnati. Idan muka duba Aikin Gwamnati yayi wahala kwarai, amma noma kam Ubangiji yana saukar da ruwa ba tare da bambance gonar wane da wane ba. Kowa dai na iya yin aikin gona, ko kuwa Mutum ya shiga kasuwanci dsr. Idan har muka fahimci cewa babu wanda zai yi mana shikenan, haka neman Dukiya ta ke. Mu sani cewa kasuwanci har Allah SWT ya hada sa da Ibadar Allah. Manzon SAW kuwa yana cewa: Dan Kasuwa Mai gaskiya-Amintacce, yana tare da Shahidai a Ranar Kiyama.
To ‘Yan uwa Musulmi, wannan kenan. Amma abin da za ayi magana a kai da karfafawa shine noma. Dole mu fuskanci wannan harka ta noma musamman a irin wannan lokaci; Muna fama da matsalar tattalin arziki, ga kuma Jama’a, ga filin noma ga kuma ruwan sama. Sai dai ya zama babu wannan zuciyar a yanzu, duk da cewa Iyayen mu da noma suka taso. Kai bari ma, ba nan kadai ba, kaf Kasar nan, an ci da ita da arzikin noman auduga da gyada dsr, mun san wannan. Yanzu an bar wannan an komawa wani abu dabam duk da Allah SWT yana nuna mana albarkar noma. Babu wani haraji da ake biya na ruwan sama domin noma, ya rage ka tona Kasa, ka shuka, sai a samu tsiro da izinin Allah. Allah SWT ne yake cewa ya mana tanadi tare da gonakin mu a cikin Al-Kur’ani.
‘Yan uwa Musulmi, muyi tunani da irin abubuwan da ke faruwa a Kasar nan. Ka da mu zama ci ma zaune; mu zama sai dai a sayo kaya daga Kasashen waje domin mu ci. Yaushe Mutum zai kashe dan albashin sa wajen sayan shinkafa? Da ace Mutum zai noma ta, da zai sami abin da zai ci tare da Iyalin sa, har ya ba wasu, yana mai fitar da Zakka don Allah SWT yace Arziki ne ga Bayin Sa.
Ya kamata Gwamnonin mu na Arewa suyi tunani, su duba su ga abin da ya faru tsakanin Jihar Kebbi da Jihar Legas. Yanzu haka ana sayar da buhun shinkafa ta Kebbi kan kudi N12, 000 a Jihar Legas. Meyasa sauran Jihohin mu ba za su yi haka ba? Me zai hana Sokoto da Zamfara su hada kai? Me zai hana Jihohin Kano da Katsina, ko Kaduna da Neja, ko Yobe da Borno, da su Bauchi da Gombe? Idan har aka yi haka mun daina maganar shigo da abinci daga Kasar waje. Ya kamata mu lura da wannan, ka da mu zama ci-ma zaune. Koa bin kunya ka ga ana sayar da hatsin da muka noma ga masu giya. Daga karshe aje ayi giya, Direbobi su sha, ayi ta kashe Mutane a hanya.
Wannan dai matashiya ce, kuma lallai ba mu makara ba. Muna sa ran cewa zuwa shekara mai zuwa za a samu karin yawan masu noma da amfanin gona ba tare da mun dogara daga Kasashen waje ba.
Allah ka shiryar da mu da Shugabannin mu, ya sa mu cika da Imani.
Ameen.



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi


3 comments:

  1. Allah ya bamu ikon neman na kanmu ya kuma ciyar da mu daga halal. Mun gode Mal Mamman

    ReplyDelete
  2. Allah ya bamu ikon neman na kanmu ya kuma ciyar da mu daga halal. Mun gode Mal Mamman

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...