Tuesday, January 31, 2017

Malaman Makarantun ‘Foli’ sun shiga yajin aiki



Kungiyar ASUP tace babu wani ja da baya a kokarin ta na shiga yajin aiki


Gwamnatin tarayya dai tayi kokarin a sasanta amma abin ya ci tura


Sai dai wasu Makarantun sun ki shiga yajin aikin






Mr. Anderson Ezeibe, wanda shine Sakataren Kungiyar ASUP ta Malaman Makarantun Polythechnic yace sun tafi yajin aiki na mako daya kuma babu maganar ja da baya a kan batun na su.

Malaman Makarantun na gaba da Sakandare sun tafi yajin aikin ne a tsakar daren jiya bayan duk wani yunkuri sasanci da Gwamnati ya ci tura. Kungiyar tace kaf ma’aikatan na ta za su janye aiki har sai wa’adin ya kare.




Kungiyar za ta tafi yajin aikin mako guda ne a matsayin gargadi kafin idan abubuwa sun dace su dawo, idan kuma ba haka ba to sai baba ta gani. Tun bara dai Kungiyar ta ke kukan za ta tafi yajin aiki, sai dai Kungiyar tace Gwamnati ba tayi komai ba.

Kungiyar tace kowace Makaranta tana cikin yajin, to sai dai ga shi Makarantar Polythechnic ta Jihar Kaduna ba ta bi sahu ba.


[NAIJ Hausa]

Ya za a kare da Shugaba Trump na Amurka?


– Sabon Shugaban Kasar Amurka zai fuskanci kalubale game da sababbin tsare-tsaren sa


Tuni Kasashen Duniya sun fara nuna Trump da karamin yatsa


Ko za a kwashe da Trump lafiya kuwa?




Idan ana bin labarai dai an san cewa a Ranar Juma’ar da ta gabata ne, Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya nemi a hana baki da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar Amurka. Trump ya nemi ya hana Kasashe 7 na Musulmai shiga cikin Kasar.

Sai dai Jama’a da dama sun soki wannan tsari, suna ganin ba zai yi wani tasirin kirki ba, wasu ma suna ganin cewa akwai munafunci a tsarin na Trump. Mutanen Amurka sun ta buga zanga-zanga, daga baya kuma aka samu wata Kotu ta bada umarnin dakatar da tsarin na Trump. Bugu da kari ma dai Shugaba Trump din ya kori Atoni-Janar na Kasar bayan ta ki kare tsarin na sa na korar baki.


A Jiya ma dai Tsohon Shugaban Kasar, Barrack Obama yace sam bai yarda da wannan tsari na Trump ba, ko ta kusa ko ta nesa. Kwanan nan ne dai wani Tsohon Dan wasa Mo Farah ya soki Shugaban Kasar da wannan manufar.

A baya dai Sanatoci da ‘Yan Majalisun Kasar na Jam’iyyar Democrats sun nemi zama domin nuna adawar su da wannan doka. Dama wasu dai na ganin cewa daga karshe dai tsige Donald Trump din za ayi tun kafin ya je ko ina.





[NAIJ Hausa]

An bankado wani laifin su Saraki da Dogara



Ta kwabe da Shugabannin Majalisar Kasar nan a halin yanzu


– Wata Kungiya ta bankado barnar da su Saraki suka yi da sunan gidajen haya


Ana zargin Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Mataimakan sa da yin sama da wasu Miliyan 600






Ana zargin Shugabannin Majalisar Kasar nan da yin gaba da wasu kudi sama da Naira Miliyan 600. Kamar dai yadda Sahara Reporters ta fada akwai hannun shi Bukola Saraki da Mataimakin sa; Ike Ekeremadu da kuma Yakubu Dogara da na sa Mataimakin; Yusuf Lasun.

Wata Kungiya mai suna CATBAN ce ta zargi Shugabannin Majalisar Dattawa da Wakilan Tarayyar Kasar da matsawa Hukumar FCDA mai kula da harkokin Birnin-Tarayya Abuja har sai da aka ba su gidajen kwana bayan kuma Gwamnati ta basu kudin gida.

Hukumar ta FCDA mai kula da cigaban Birnin-Tarayyar tace dai ta kashe kudi har N630,125,499.90 domin kamawa manyan ‘Yan Majalisar haya da kuma gyaran gidajen da aka kaman. Sai dai ashe ‘Yan Majalisun suna zaune cikin gidajen su na kan su ne, sai suka karkatar da kudin da aka ware na hayan su saka a aljihu abin su.


[NAIJ Hausa]

Da alamu Gwamnan Kaduna bai zo da wasa ba



Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya nuna ba da wasa yake ba


Gwamnan yace duk Kwamishinan da ba zai iya ba, ya sauka


El-Rufa’i ya shirya kammala duk wasu manyan ayyuka a wannan shekarar





Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya nuna ba fa wasa ya fito yi ba. Gwamnan yayi kira ga mukarraban sa yace duk wanda ba zai iya ba ya ba shi wuri. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a zaman da Gwamnatin Jihar tayi na dabbaga ayyukan wannan shekarar.

Mai Girma Gwamnan ya sha alwashin kammala duk wasu manyan ayyuka da ya dauko a wannan shekarar, ya bayyyana haka ne a wannan taron da Gwamnatin Jihar da Ma’aikatar kasafin kudi su ka hada na kwanaki 2 a jere. Gwamnan ya duba ayyuka da kuren da suka yi a shekarar da ta wuce da niyyar a gyara su wannan shekara.





Gwamna El-Rufa’i yace daga yanzu dole kowace Ma’aikata ta rika kirkiro manyan ayyukan gina Jiha, ya kuma bada umarni kowane Kwamishina ya rika fita yana duba ayyukan da Jiha ta ke yi. Gwamnan yace daga yanzu zama cikin Ofis ya karewa Kwamishinoni.

Malam Nasiru dai yace duk Ma’aikatar da ba ta kawo kudi, ba za ta ga kudi ba a kwaryar ta. Don haka ne ma Gwamnan yace duk Kwamishinan da ba zai iya tatso akalla Miliyan 10 a wata ba ya tafi gida. Gwamnatin dai tana da kwanaki kusan 850 ta cika alkawuran da ta dauka Inji Kwamishina Muhammad Sani Dattijo.




 [NAIJ Hausa]

Monday, January 30, 2017

An takawa Donald Trump burki


– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya bada umarnin hana wasu baki shigowa Kasar Amurka


– Sai dai kuma Kotu ta dakatar da wannan shiri na Shugaban Kasar


Wasu Kasashen sun fara maida martani




Kwanan nan, sabon shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya saka hannu kan wata doka da ta hana baki shiga cikin Kasar Amurkar. Hakan dai ya sa aka tsare mutane kusan 200 da suke kokarin shigowa a filin jirgi.

Wata Kotu da ke Brooklyn ce dai ta cece Jama’a, inda wani Alkali ya hana dabbaga wannan doka ta sabon shugaban Kasa Donald Trump. Wannan doka dai ta Donald Trump ta shafi har wadanda suke dauke da katin zama ‘Yan Kasar Amurka. 


Ana ta zanga-zanga a Amurka, wasu ma na shirin neman rabewa daga Kasar


A Ranar Juma’a Donald Trump dai ya nemi a hana bakin da ‘yan gudun hijira shigowa cikin Kasar na watanni hudu yayin da ya kuma haramtawa ‘Yan Kasar Siriya shigowa Amurkar har abada. Kasar Iran dai wannan abu bai yi mata dadi ba, kuma ta fara shirin hana Amurkawa shigan Kasar.

A wani harsashe da NAIJ.com tayi, an fahimci cewa ‘Yan Najeriya masu takardar shaidar zama ‘yan wata Kasar na iya fuskantar kalubale musamman idan dayar Kasar ta su tana cikin guda 7 da Trump ya hana shiga Amurka.


[NAIJ Hausa]

An kusa kashe wani Direba don yace Buhari ya rasu


– Wani Mutumin Jihar Kano ya kashe wani Direba da mari don yace Buhari ya rasu


– Har yanzu dai wannan Direba bai san inda yake ba


– Ana ta yada rade-radin cewa Shugaba Buhari ya rasu a Asibiti





Kamar yadda Jaridar Vanguard ta fada, wani mutumi mai suna Usman Bukar ya yankawa wani Direban mota mari har sai da ya kusa mutuwa don kuwa yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mutu.

Wannan abu dai ya faru ne a Jihar Delta tsakanin Direban motar haya da wani matashi mutumin Kano. Wanda abin ya faru a gaban say ace mutumin ya yankawa Direban mari ne bayan ya ji yana yada labarin cewa Shugaba Buhari ya rasu a wurin ‘yan jarida.




Wannan mutumi dai yace za a jefa gawar Shugaba Buhari a Kogin Neja domin halittun ruwa su ci, ya kara da cewa Shugaba Buhari mugun mutum ne, nan ne fa Malam Usman ya harzuka, ya ketawa wannan mutumi wani mugun mari, yanzu haka yana can wani asibiti mai suna Temple Clinic da ke Garin Asaba.

‘Yan uwan wannan mutumi dai sun nemi rama abin da ya faru, sai dai Jami’an ‘Yan Sanda sun shiga tsakani. Andrew Aniamaka, mai magana da bakin Hukumar ‘Yan Sanda ya tabbatar da faruwar wannan abu. Yanzu haka Usman na hannu Jami’an tsaro shi kuma wannan Direba na can Asibiti bai san halin da yake ciki ba.


[NAIJ Hausa]

Sunday, January 29, 2017

Ba mu da shirin kara kudin man fetur-Inji ‘Yan kasuwa


Masu jigilar mai sun tabbatar da cewa babu maganar kara farashin man fetur


‘Yan kasuwan sun ce babu wannan shiri a yanzu


Kwanaki aka fara jitar-jitar watakila farashin fetur zai tashi





Kungiyar masu jigilar main a Kasar nan ta bayyana cewa babu maganar karin farashin kudin man fetur. Kungiyar ta IPMAN na bangaren Kano tace Jama’a su daina daukar maganar cewa kudin mai zai daga.

Alhaji Bashir Dan Malam wanda shine Shugaban Kungiyar ta IPMAN a Kano yace za a kama duk wadanda suka sayar da mai a sama da farashin da Gwamnati ta saka. A Kano dai cikin ‘yan kwanakin nan mun samu labarin ana sayar da litan man fetur har a kan N155.

Dan Malam ya fadawa Hukumar Dillacin labarai cewa babu wani shiri na kara farashin man fetur din. Shugaban Kungiyar yace jita-jita ne kurum maras tushe. Dan Malam yace sun zauna da Gwamnati sun kuma shawo kan sabanin da suka samu na kudin don haka farashin mai na nan yadda aka sani.

Kwanaki NNPC dai suka ce man da su ke da shi a ajiye zai isa Najeriya har na fiye da wata guda. Matatar man Najeriya duk sun fara aiki don haka babu maganar a samu karancin kanaziri ko man babbar mota.


[NAIJ Hausa]

Ina na kan baka na, Inji Faston da yace a kashe Fulani


– Fasto Johnson Sulaiman yayi kira ga Mabiyan sa da su kashe Makiyaya Fulani kwanakin baya


– Faston yace duk Makiyayin da aka gani kusa da Cocin sa a aika sa Lahira


– Har yanzu dai yace ba zai nemi gafarar abin da ya fada ba


– Fasto Johnson yace ba fada yake da Hausa/Fulani ba




Fasto Johnson Sulaiman na cocin na Omega Fire ya ba Mabiyan sa umarnin kashe duk wani Makiyayi da aka gani kusa da Cocin sa. Faston yace a yanka masu wuya nan take, sai dai wadannan kalamai sun nemi su tada Kasar.

Faston yace ba zai nemi gafarar kowa ba, Faston ya fadi haka ne a wata huduba da yayi wa Mabiyan na sa. Faston dai yace ba fada yake da Fulani ko Hausawa ba, ya kira su mutanen kirki masu matukar hakuri.

Shi dai Faston yace idan har aka ga wani Bafullatani ya shigo cikin cocin na sa ko da wasa ne a aika sa lahira. Faston yace don kuwa Fulani suna kashe Kiristoci a fadin Kasar babu abin da kuma aka yi, don haka su ma za su yi hakan.

Hukumar DSS dai ta nemi ta cafke Fasto Sulaiman bayan yayi wannan kalamai, Gwamna Fayose na Ekiti yayi wuf ya je ya hana. Tun bayan nan ne kuma Gwamna Fayose ya zama Direban Faston.


[NAIJ Hausa]





Mutumin da ya auri mata kusan 100 ya mutu



Mai mata 100 ya mutu; yayi wasiyya a daina zina



Bello Abubakar Masaba, mutumin da ya auri mata barkatai ya riga mu gidan gaskiya


Bello Masaba ya mutu yana da mata kusan 100


– Bello Masaba ya rasu yana da shekaru 93




Idan ba a manta ba akwai wani ta’aliki mai suna Bello Abubakar Masaba, wani mutumin Bida ta Jihar Neja mai mata barkatai. Wannan mutumi dai yanzu Allah yayi masa cikawa a jiya Asabar bayan yayi ‘yar gajerar rashin lafiya.

Masaba dai ya yanke jinki ya fadi har sau biyu, daga karshen yace ga garin ku. Wata Jarida mai suna The Eagle ta bada labarin rasuwar wannan mutumi. Alhaji Mutairu Salahuddeen; wani mai magana a madadin dangin wannan mutumi ya tabbatar da haka.





Bello Masaba dai kowa ya san sa da yawan mata, ace mai mata 97, yayi mata kusan guda 107, ya kuma rasu ya bar fiye da 80, bayan ya rabu da wasu da dama. Ya haifi ‘ya ‘ya sama da 185, sai dai wasu sun rasu, yanzu ya bar akalla guda 133.

Bello Masaba dai ya rasu ne jiya da rana, an kuma shirya jana’izar sa a Ranar yau da safe. Marigayin yayi wasiyya da a daina zinace-zinace a koma auren mata na addini. Masaba ya mutu yana da shekaru 93.


[NAIJ Hausa]

Friday, January 27, 2017

Amurka tana da labarin za ayi wa Buhari juyin mulki


Ashe Kasar Amurka tana da labarin za a kifar da Gwamnatin Buhari a 1985


Babangida IBB ya kifar da Gwamnatin Buhari a wani juyin mulki


Ashe CIA ta Amurka ta san duk abin da zai faru





Wasu bayanan sirri da muke samu daga Hukumar bincike ta Amurka watau CIA sun nuna cewa ashe Kasar Amurka tana da masaniyar cewa za a hambarar da Gwamnatin Janar Buhari shekaru 30 da suka wuce.

CIA tana da labarin wanda zai kifar da Gwamnatin Janar Buhari da kuma lokacin da za a yi wannan juyin mulki. CIA ta gano cewa za a yi wa Buhari juyin mulki a shekarar 1985 lokacin da tattalin arzikin Kasar da kuma goyon bayan wasu ya fara tabarbarewa.

An dai samu rashin jituwa a tsakanin Sojojin Kasar musamman kanana da suka fito daga Kudancin Kasar lokacin Janar Buhari yana mulkin Soji. Tun lokacin dai CIA tace ba za a dade ba, za a kifar da Gwamnatin sa.

A jiya kuma Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa hutu ya kai Shugaba Buhari Landan ba ganin Likita ba. Femi Adesina; Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai yace yanzu haka Shugaba Buhari ba ya wani Asibiti.


[NAIJ Hausa]

Sabon shugaban Gambia ya dawo gida


Sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya dawo gida


– Adama Barrow ya shigo Kasar sa bayan Yahaya Jammeh ya fita


– Barrow ya baro Kasar Sanagal inda ya labe




Sabon shugaban Kasar Gambia da aka zaba a karshen bara, Adama Barrow ya taba Kasar Gambia. A jiya ne Barrow ya shigo Garin Banjul na Kasar ta Gambia, bayan da shi kuma Yahaya Jammeh ya bar Kasar.

Kamar yadda BBC ta fada, Jama’a sun yi dafifi a filin jirgi inda suke jiran sabon shugaban na su Adama Barrow ya iso. Barrow dai ya dade a labe a Kasar Senegal tun bayan da aka zabe sa, kafin a rantsar da shi.

An dai ga Sojojin Najeriya suna sintitiri yayin da Barrow ya shigo Kasar. Dakarun ECOWAS dai suka matsawa Jammeh har sai da ya sauka daga mulkin bayan ya fadi zabe, ba dan yana so ba. Jammeh ya fi shekaru 20 yana mulkin Kasar Gambia.

Da alamu dai tsohon Shugaban Kasar Gambia, Yahaya Jammeh zai cigaba da rayuwar jin dadi ne ko a zaman gudun hijirar da zai yi. An dai bar Jammeh ya tafi da ingaramammun motocin har guda 13 zuwa Kasar Equatorial Guinea inda zai yi zaman san a Gudun Hijira.



[NAIJ Hausa]





Ta kashe kan ta bayan MMM sun sha ta misilla


– Wata mata ta kashe kan bayan ta ci bashi banki ta zuba a MMM


– Wannan mata dai tana da ‘ya ‘ya har biyu


– Wannan abu ya faru ne a Garin Makurdi na Jihar Benue





MMM dai yayi sanadiyar mutuwar wata mata mai shekaru 34 a Garin Makurdi da ke cikin Jihar Benue. Wannan mata dai mai suna Gloria Samson tana da ‘Ya ‘ya har biyu.

Abon dai da ya faru shine wannan mata ta ci wasu tarin bashi har wurare hudu, bayan nan kuwa ta zuba wannan kudi a cikin tsarin nan na MMM tana mai sa ran ta ja kaya, ko da tayi haka kenan sai aka rufe tsarin a karshen wancan shekarar. Shi ke nan fa aka sha ta misilla!

Wannan mata dai ta bar gida a karshen Disamba ta jefa kan ta cikin rafi, sai dai gawar ta ‘Yan Sanda suka gani bayan ‘yan kwanaki. Wannan mata dai sai da ta nemi gafarar ‘ya ‘yan ta biyu kafin ta jefa kan ta cikin rafin. Marigayiyar dai ta ci bashin banki har kimanin N400, 000 ta jefa cikin MMM.


[NAIJ Hausa]



Thursday, January 26, 2017

An shiga uku: Trump ya fara fatattako 'Yan Afrika


– Sabon Shugaban Kasar Amurka ya fara koro bakaken Afrika da suka tare Amurka gida


Trump ya sa kafar wando daya da bakin haure


Donald Trump kuma ya fara shirin gina katangar karfe tsakanin sa da makwabta





Sabon shugaban Kasar Amruka, Donald Trump ya sha alwashin kare kaimi wajen bakin iyakokin Kasar Amurka saboda masu shigowa su tare a Kasar ba a san da su ba. Yanzu haka dai har Trump ya fatattako ‘Yan Afrika kusa 100 gida.

A Ranar Laraba ta Jiya sabon shugaban Kasar ya fatattako bakin haure a Kasar har guda 92. A Ranar ne kuma Shugaba Trump din ya fara shirin gina katangar karfe tsakanin Kasar Amurka da makwabta Kasar Mexico.

Cikin wanda Trump ya koro akwai mutanen Kasar Somalia, da kuma Kenya, wadanda aka tusa keyarsu har filin jirgi. Har wa yau dai sabon Shugaban ya hana a bada takardar shiga Kasar Amurka ga mutanen Kasar Yemen, Iraki, Iran, Somaliya, Sudan, da kuma Kasar Siriya.

Har wa yau kuma Kasar Amurka na shirin aika Dalibai zuwa Duniyar wata domin su girka giya kamar dai yadda muka samu labarai daga Birnin Los Angeles na Kasar Amurka. Wannan ne dai karo na farko a tarihi da Amurka tayi irin wannan abu.


[NAIJ Hausa]

Amurka za ta aika Dalibai Duniyar wata domin su girka giya



– Kasar Amurka na shirin aika Dalabai zuwa Duniyar wata


– Za ayi kokarin girka giya a cikin wata idan an je


Donald Trump kuma ya fara shirin gina katangar karfe





Kasar Amurka na shirin aika Dalibai zuwa Duniyar wata domin su girka giya kamar dai yadda muka samu labarai daga Birnin Los Angeles na Kasar Amurka. Wannan ne dai karo na farko a tarihi da Amurka tayi irin wannan abu. 

Daliban Jami’ar California da ke Garin San Diego suna cikin wata gasar zuwa Duniya wata. Zuwa karshen wannan shekarar dai za a aika jirgi zuwa sararain samaniya inda zai je Duniyar wata.

Saboda bincike dai Daliban za su yo kokarin girka giya a saman watan domin ganin yadda abubuwa suke gudana a Duniyar. Wannan dalibai suna daga cikin Dalibai sama da 3000 da aka zaba domin su je Duniyar wata. An dai zabi Dalibai 25 ne kacal a Gasar.




[NAIJ Hausa]

Wai da gaske ne Osinbajo zai sauka?


Ofishin Mataimakin shugaban kasa ya karyata rade-radin cewa ana nema a tursasa Osinbajo yayi murabus


Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa yayi bayani


Sanata Ojudu yace wannan karyar banza ce





Ana ta yada rade-radin cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na shirin ajiye aiki bayan matsin lamba da yake samu. Fadar Shugaban Kasa dai ta yi wuf ta maida martani ga masu yada jita-jitar inda tace sam karyar banza ce ba gaskiya ba.

Mai ba Shugaban kasa shawara a game da harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu yayi jawabi daga Fadar Shugaban kasar. Sanata Ojudu ya bayyanawa Jaridar Punch cewa rade-radun da ke yawo ba gaskiya bane. Rahotanni sun bayyana a baya cewa wasu Gwamnoni na neman tursasa Osinbajo yayi murabus.

Sanata Ojudu yace babu kanshin gaskiya ko na sisin kwabo a cikin maganar. Yanzu haka dai Mataimakin Shugaban kasar ne ke rike da Kasar a matsayin mukaddashi. Kuma yana kan aiki ba dare ba rana.



[NAIJ Hausa]

Wednesday, January 25, 2017

Sanata Shehu Sani ya karyata Fadar Shugaban Kasa


Sanata Shehu Sani yace sam ba Shugaba Buhari ya rubuta wasikar da ta wanke Babachir ba


A wasikar da aka maido wa Sanatocin martani jiya, shugaban kasa ya wanke Babachir Lawal


Shehu Sani yace an yi jana’izar yaki da rashawa




Sanata Shehu Sani mai wakiltar Yankin tsakiyar Kaduna yayi tir tare da mamaki ga martanin wasikar da aka samu daga fadar Shugaban kasa inda aka wanke Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal daga dukkan zargi.

Shehu Sani yace Fadar Shugaban Kasa tayi karya a wasikar ta, Sanatan yace ba shakka sun gayyaci Sakataren Gwamnatin domin ya kare kan sa a Majalisar. Haka kuma Sanatan da ya gudanar da bincike game da Sakataren yace kusan ‘yan kwamitin na sa, sun sa hannu a takardar da ya gabatar ba kamar yadda wasikar Shugaban Kasa ta fada ba.


Shehu Sani dai yayi mamakin yadda Fadar Shugaban Kasa tayi mursisi ta hau kujerar naki game da rokon da aka yi na tsige Sakataren Gwamnati, Babachir David Lawal bisa zargin mikawa Kamfanin sa wasu kwangila.

Shehu Sani yace yanzu an yi jana’izar yaki da cin hanci da rashawa a Gwamnatin Shugaba Buhari. Don kuwa ana tsince wadanda za a bincika ne da laifi a Mulkin na Buhari.



[NAIJ Hausa]

Tuesday, January 24, 2017

Za a fara aikin jirgin kasa Legas zuwa Ibadan


Gwamnati ta saki makudan Biliyoyi domin aikin jirgin kasa





Rahotanni daga Jaridar Punch sun nuna cewa Gwamnatin tarayya ta saki kudi har Naira Biliyan 72 domin shirin fara aikin jirgin kasa Legas zuwa Ibadan. Ministan sufuri na Kasar, Rotimi Amaechi ya tabbatar da wannan jiya.

Minista Rotimi Amaechi yace wannan yana cikin bangaren kudin da za ayi amfani da su wajen zamanantar da hanyar jirgin kasar. Ministan yace aiki za a fara gadan-gadan ba tare da wata-wata ba kuwa.

Wannan ne dai karo na farko da aka fitar da irin wannan mahaukatan kudi domin wani aiki. Amaechi ya roki Majalisar Kasar ta taimaka ta amince da rokon Shugaba Muhammadu Buhari na ciwo bashin dala biliyan 30.

A taron Gwamnatin tarayya ta fitar da wasu hanyoyi har guda 59 da za su fitar da Kasar daga halin da ake ciki na matsin tattalin arziki. Minista Udo Udoma ya bayyana hakan, daga ciki akwai dawo da akala kan abubuwan da ba su shafi man fetur ba irin su noma da ma’adanai.




[NAIJ Hausa]


Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...