Za
a haramtawa wasu salula whatsapp
– Miliyoyin wayoyi za su daina amfani da whatsapp
– Daga karshen shekarar nan, za a haramtawa wasu salula whatsapp
– Wayoyi na kirar Android, Windows da IOS za su gamu da matsala
Wayoyin salula da dama irin
na zamani za su gamu da cikas zuwa karshen wannan watan na Disamba. Za a
haramtawa wayoyi da dama amfani da kafar sadarwa ta whatsapp kawo karshen
wannan shekarar.
Gidan Facebook ne dai suka
saye kamfanin whatsapp a kwanakin baya, Miliyoyin mutane dai kuwa suna amfani
da kafar whatsapp wajen aika sakonni. Sai dai masu wayoyi irin na da; kamar su
Windows, Android da IOS ba za su samu damar cigaba da amfani da whatsapp ba.
Whatsapp din tace tsofaffin
wayoyin ba za su iya cigaba da amfani da manhajar ba, watakila har sai nan da
zuwa shekarar mai zuwa. Wayoyi irin su Apple da tsofaffin Android za su bar
whatsapp.
Haka nan ma kuwa, masu wayar
Blackberry da Nokia za su gamu da babban cikas na amfani da manhajar whatsapp
har sai nan da tsakiyar shekara mai zuwa. An dai dade ana amfani da whatsapp
wajen aika sakonni.
No comments:
Post a Comment