– Jami’ar WAEC ya bayyana cewa ashe mafi yawanci makafi satar amsa suke yi lokacin jarrabawa
– Misis Francis Iweha-Onukwu tace rashin kintsi ke jawo
haka
– An kira Gwamnati ta kara karfi wajen harkar ilmi
Wata Jami’ar Jarrabawar WAEC
ta Yammacin Afrika, ta bayyana cewa ashe mafi yawanci makafi masu rubuta
jarrabwar, satar amsa suke yi domin su samu nasara. Jami’ar tace hakan na
bayuwa ne saboda rashin shiryawa Jarrabawar da kyau.
An dai kira Gwamnatin Kasar
ta kara karfi wajen harkar ilmi gaba daya. Hukumar Jarrabawar tace mafi
yawanci, Makafi kan hada kai da ‘Yan uwan su ne suyi satar amsa a Jarrabawar.
Jami’ar ta bayyana haka ne ga Manema labarai a jiya Laraba.
Hukumar Jarrabawar tace
dalilin da ka jawo haka shine rashin shiri da kayan aiki da dalibai makafin
suka rasa. An kira Gwamnati ta dage wajen harkar ilmin nakasassu da marasa
karfi. Idan har Gwamnati ta sa karfi, ba shakka irin wannan dalibai suna da
baiwar karatu, Inji ta.
Kwanan aka samu labarin wata
mata da tayi shekaru 30 tana sana’ar
abinci, da haka ta biyawa dan nan na ta kudin makaranta. Tun daga Ajin Nursery har ya kammala Sakandare inda ya
rubuta jarrabawar WAEC. Wannan yaro dai yace uwar sa ce uban sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment