Sunday, December 25, 2016

‘Yan Sanda sun tasa Gwamna Wike a gaba

  Hukumar ‘Yan Sanda tace za ta dauko Turawa domin su tantance muryar Gwamna Wike


Ana dai ta binciken abin da ya wakana na magudi a Jihar Rivers


Hukumar ‘Yan Sanda tace za tayi iyaka kokarin ta wajen ganin an yi gaskiya




Jami’an Tsaro sun nemi taimakon wasu kwararru daga Kasar waje domin su taya su binciken sautin da aka samu na Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike inda yake kokarin murde zabe da ma alwashin kashe wani Jami’in zaben a wayar tarho.

Cikin makon nan da ya gabata ne Sufeta na ‘Yan Sanda, Ibrahim K. Idris ya bayyana haka. Sufetan ya koka da rashin Jami’an san a ‘Yan Sanda a wajen zaben, yace hakan ba zai kara faruwa a Kasar nan ba.

Dama can mun rahoto cewa Hukumar ‘Yan Sanda na Kasar ta nada kwamitin da ke dauke da wani kwararre a harkar irin wannan binciken. Za a gabatar da wannan aiki cikin wata guda, kuma a fitar da sakamako.

Sai dai Gwamna Wike yace can su ji da shi. Hukumar DSS ma ta zarge sa da yunkurin tada zaune-tsaye a Birnin Tarayyar Abuja. Gwamnan dai yace Jami’an tsaron ba su yi masa adalci kuma suna kokarin kare Ministan Buhari, Rotimi Amaechi.
 



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...