Tuesday, December 6, 2016

Kwastam ta haramta shigo da motoci


Gwamnatin Tarayya ta haramta shigo da motoci ta Kasa cikin Najeriya

 

Kwastam tace duk mai mota a bakin iyaka ya shigo da ita kafin sabuwar shekara mai zuwa

 

– Daga karshen watan nan, babu damar shigo da motoci kowace iri sai ta iyakar teku




Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin Kasar nan ta iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da tsofaffin motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya.

Hukumar Kwastam tace daga Junairun shekara mai zuwa, babu damar shigo da motoci ta kan iyakar Kasa. Za a bari ne a rika shigo da motoci kawai ta iyakar ruwa. A Watan Afrilun shekarar nan ma dai aka haramta shigowa da shinkafa ta iyakar Kasa. 


Jami’in sadarwa na Hukumar Kwastam din, Mista Adeniyi Wale ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar da kuma sa hannun Shugaban Kwastam din na Kasa, Hameed Ali. An nemi duk wani mai motoci a kan iyaka ya shigo da su kafin karshen wannan watan na Disamba. 

Kwanakin baya Majalisar Dattawa ta fara kokarin hana shigo da motocin da ba sababbi ba cikin Kasar.

[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...