Thursday, December 22, 2016

Watakila karshen Babachir ya zo



Da alamu kwanakin Babachir David Lawal a matsayin Sakataren Gwamnati sun zo karshe


Akwai yiwuwar Shugaba Buhari ya fara neman wadanda za sum aye gurbin sa


Ana zargin Sakataren Gwamnatin Kasar da wasu laifuffuka




Rahotanni na nuna cewa Shugaba Buhari ya fara cigiyar Sabon Sakataren gwamnatin tarayya wanda zai maye gurbin Babachir David Lawal. Majalisar Dattawa dai ta jefawa Mista Babachir din kashi dumu-dumu a jika.

Jaridar Daily Post ce dai ta kawo wannan rahoto. Shugaban Kasar dai ya fara neman wanda zai zama sabon Sakataren Gwamnati. A Ranar Larabar nan wani da ke Fadar Shugaban Kasa ya bayyana cewa an fara bidar sabon Sakatare.





Majiyar ta nuna cewa cikin wadanda ake sa rai su canji Sakataren, akwai Audu Ogbeh wanda shine Ministan noma na Kasar. Akwai kuma wasu tsofaffin ma’aikatan Gwamnati da ake tuntuba domin su canji Babachir din.

Ko a shekaran jiya dai Wani Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Kasar nan, Adolphus Wabara, ya kira Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya sauka daga matsayin sa saboda tarin zargin da ke kan sa.


A biyo mu a shafin mu na NaijComHausa


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...