– Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika shekaru 74 a Duniya Ranar Asabar
– Mutane da dama sun aika sakon gaisuwar su ga Shugaban Kasar
– Sai dai ba a ga Matar Shugaban Kasar da ma Mataimakin Shugaban ba a wajen Bikin
An nemi Aisha Buhari an rasa wajen Bikin murnar zagayowar Buhari
A
karshen makon nan ne Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru
74 a Duniya. Mutane da dama na Kasar sun taya Shugaban na su murna daga fadin
Kasar. Ko da dai ana ta fama da matsalar tattalin arziki a Kasar.
Sai
dai wani abin mamaki, ba a ga Matar Shugaban Kasar, Hajiya Aisha Buhari wajen
bikin murnar cika shekarun Shugaban Kasar ba. Haka kuma Mataimakin Shugaban
Kasar ba ya wajen wannan Biki.
Sauran
Shugabannin Majalisa ma dai ba su samu zuwa wajen wannan Biki ba. A shekarar
bara kuwa, Mutane da dama; Ministoci da sauran Manyan Gwamnatin sun halarci
Bikin a Fadar Shugaban Kasar.
An
dai yi fareti na Soji, sannan aka mikawa Shugaban Kasar wani katafaren katin
taya sa murna. Tsohon Shugaban Kasa, Dr. Jonathan Ebele Goodluck da sauran
manyan Kasar sun taya Shugaban murna tare da yi masa addu’a.
Wannan makon ne dai Shugaban Kasar ya aurar da
Diyar sa, Zahara Buhari ga Ahmed Muhammad Indimi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment