– Ana yunkurin haramta sanya dogon Hijabi a Kasar Jamus
– Shugaban Kasar Jamus na kokarin haramta amfani da Hijabi
– Hakan zai kawo raguwar Musulmai a Kasar
Jaridar
Daily Mail ta rahoto cewa ana yunkurin hana amfani da dogon Hijabi da ake kira
burqah a Kasar Jamus.
Shugaban
Kasar Jamus, Angela Merkel tace Jamus Kasar Kirista ce don haka bai dace ace
ana amfani da dogon Hijabi ba watau burqah. Shugaban Kasar ta bayyana haka ne a
wajen wani Taron Jam’iyyar su ta CDU da aka gudanar.
Shugaban
Kasar tace za tayi kokarin hana Musulmai dindirinzo zuwa Kasar Jamus din. Tace
ba za a maimaita irin abin da ya faru a Kasar ba shekarar bara lokacin da
Musulmai suka yi ta Hijira suna shigowa Kasar.
Jam’iyyar
CDU ta su Angela Merkel ta fadi zaben Jihohi da aka yi saboda matsayar ta game
da Musulmai da suke shigowa Kasar. Kusan Musulmai 890,000 suka shigo Kasar
Jamus da ke Tsakiyar Turai shekarar bara.
[Daga NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment