Wednesday, December 14, 2016

Da Jami'an tsaro muka yi takara ba APC ba-Inji PDP

 

PDP tace APC ta bayyana yadda APC tayi amfani da Jami’an tsaro wajen magudi a zaben Rivers

 


PDP tace Hukumar INEC ta nuna bambamci

 


Jam’iyyar PDP tace da Gwamnatin Tarayya tayi takara ba APC ba

 


Jam’iyyar PDP tace an yi amfani da Jami’an Sojoji wajen yin magudi na Inna-na-naha a Zaben Rivers. Bangaren Ahmed Makarfi na PDP suka ce APC ta tafka mugun magudi a zaben da ya gudana cikin kwanakin nan.  

Mai magana da bakin Jam’iyyar PDP, Dayo Adeyeye Jam’iyyar su tayi takara ne da Soji, Hukumar zabe da kuma APC. Adeyeye ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar da Birnin Abuja. APC ta samu Sanata daya ne kadai a zaben, sai dai PDP tace sam magudi aka yi har Magnus Abe yaci zaben. 


Gwamnan Jihar, Nyesom Wike ya sha alwashin cewa ba zai kara ba Jami’an tsaro wani agaji ba a Jihar sa saboda irin magudin da aka tafka da su. Gwamnan dai ya tara Jama’a inda suka tsaya tsayin-daka cewa INEC ba za ta murde masu zabe ba. 

Sai dai APC tace ba za a bugi yaro a hana sa kuka ba. PDP dai tace Gwamnatin Tarayya ce ta turo Minista, Rotimi Amaechi domin murde zaben. Sojoji dai sun ce ba su yi wani ba daidai ba a zaben. 

[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...