Wednesday, December 21, 2016

Jami’ar ABU Zaria za ta gina makarantar koyon kasuwanci




Jami’ar ABU ta Zaria za ta gina Makarantar koyon kasuwanci

 


Majalisar Jami’ar ta bada damar ayi wannan aiki

 


Akwai irin wannan Makarantar tuni a Legas


 

Jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria za ta bude Makarantar koyon kasuwanci. Majalisar Jami’ar ta amince a bude wannan Makaranta kamar yadda Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana. 

Farfesa Ibrahim Garba ne yayi wannan bayani a Jiya wajen bikin gina wani Dakin taro mai daukar mutane 300 a Jami’ar. Kungiyar ICAN ta kwarararrun Akawu na Kasar ce za ta gina wannan dakin karatu. 

Idan har an bude Makarantar Koyon kasuwancin, za a rika koyar da Ilmin Tattali da akawu da Ilmin kasuwanci har da ma Ilmin Banki na Musulunci da sauran su. Farfesa Garba yace Makarantar za ta rika bada shaidar Digirgir da Digir-digir da ma Diploma. Dama can akwai irin wannan Makaranta a Jihar Legas.

Kwanakin baya Jami’ar ta yaye dalibai masu digiri guda 11, 731. Kamar yadda muka samu labari akwai guda 2, 697 masu shaidar Digiri na biyu, sannan kuma guda 289 sun kammala karatun Digiri na uku. Akwai kusan 50 masu Digiri mai makin farko watau first class. Jami’ar Ahmadu Bello dai ita ce ta farko a Arewacin Najeriya.

[NAIJ Hausa]



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...