– An kama wani bawan Allah da laifin satar batiri na mota a Garin Ibadan
– Alkali ya aika da shi Gidan Yari na Agodi domin ya dandana kudar sa
– Mai
laifin ya amsa da bakin sa cewa ya saci batiran mota
Wani karamin Kotu da ke
Iyaganku a Garin Ibadan ya yankewa wani ta’aliki hukuncin dauri a Gidan Yari
har na watanni 3 saboda ya saci batiri na mota guda biyu. Wannan mutumi dai ya
saci batiri ne a wata mota da aka ajiye a kan hanya.
Alkali mai shari’a, Patricia
Adetuyibi tace ganin an kama wannan mutumi da laifi, kuma yana cikin wani
yanayi, ya kamata ya shiga Gidan maza domin ya dandana kudar sa ko yayi
hankali. Don haka yanzu wannan mutumi zai share watannin shida a Gidan Yarin
Agodi da ke Garin.
Wannan barawo mai suna
Akinpade Kehinde ya kasance kuma gawurtaccen dan shaye-shaye a Yankin. Wani
Jami’in ‘Yan Sanda, Philip Amusan ne ya kama sa bayan ya saci batiri mota guda
biyu wadanda kudin su ya kai N70, 000.
Akinpade ya amsa cewa lallai
ya saci batiri a Ranar 23 ga watan Nuwamba da ta wuce da safe. Bayan nan kuma
an kama sa da laifin kai hari ga wani da adda, hakan ta sa aka kara masa zaman
watanni uku a Gidan Yari.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment