– Sanatocin Kasar nan sun ce akwai matsala wajen yaki da rashawar da Shugaba Buhari yake yi
– Sanatocin sun ce karya ake yi da ake cewa su suka fi sata a Najeriya
– Sanotocin sun ce akwai wadanda Buhari ya kamata ya sanyawa ido ba su ba
Sanatocin
Kasar nan sun ce akwai matsala wajen Yaki da cin hanci da rashawa da Shugaban
Kasa Muhammadu Buhari yake yi. Sanatocin sun ce gaba daya Shugaba Buhari ya sa
ido kan wadanda ba su ke sata ba.
Wani
taron Sanatocin Kasar ne suka fadawa Jaridar Premium Times haka. Sanotocin suka
ce Masu aikin Gwamnati Buhari ya kamata ya bi, ba ‘yan siyasan Kasar ba.
Sanatocin sun yi wani Taron ‘Yan Majalisa ne a Kasar Afrika ta Kudu.
Sanotocin
sun ce aikin ma’aikatan Gwamnati ne su tabbatar da an aiwatar da kasafin kudin
Kasar, don haka su ya kamata a rika bincike ba ‘Yan siyasa ba. Wasu Sanatocin
sun musanya batun cewa sune suka fi kowa sata a Kasar, suka ce ba haka abin
yake ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment