Friday, December 23, 2016

Kungiyar CAN ta kara nuna El-Rufai da 'dan yatsa


– Kungiyar CAN tace har yanzu ba ta canza matsay ba game da Gwamnatin Jihar Kaduna


– Gwamnatin Jihar ta kawo kudirin takaita wa’azi a Jihar


– Kungiyar Kiristoci sun nanata cewa ba su fa yarda ba




Gwamnatin Jihar Kaduna ta kawo wani kudiri ga Majalisar Jihar da zai sa Gwamnati ta rika lura da sha’anin wa’azi a fadin Kasar. Kungiyar dai sun kara nanata matsayar su na cewa ba su yarda da wannan kudiri ba.

A baya ne dai Gwamnan ya tado da wannan doka wanda dama can tafi shekaru 30 a cikin dokokin Jihar. Kungiyar CAN da ma ta FPN sun maka Gwamnan a Kotu saboda yunkurin farfado da wannan doka a Jihar.

Sakataren CAN na Jihar Kaduna ya bayyanawa manema labarai a wata hira cewa har yanzu ba su amice da yunkurin takaita wa’azi ba a Jihar. CAN tace akwai lauje a cikin wannan  nadi. Ibrahim Sunday yace an shiga hakkin su. Yanzu haka dai an kai karar Gwamnan a gaban Alkali Hajarah Gwadah a Babban Kotun Jihar.

Wancan mako ne kuma dai ya bayyana cewa daga yanzu babu wani tattaki ko gangamin da ya sabawa doka a Jihar. Gwamnatin tayi wannan ne domin kawo karshen lamarin ‘Yan  Kungiyar IMN na Shi’a a Jihar Kaduna.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...