– Sarkin Ijio na Kasar Oyo ya samu rasuwa ta hanyar hadarin mota
– Mai martaba Amunijio na Ijio ya afkawa wata Gingimari ne yayin da yake tuki
– Kwanan ne dai aka kai Sarki Okunade Adegoke kara Kotu
Hadarin mota yayi sanadiyyar mutuwar wannan Oba
Mai Girma Sarkin Ijio ya rasa ran sa bayan da ya hadu da
wani hadarin mota. Sarkin yana tafiya ne inda zai koma Fadar sa cikin dare.
Sarki Okunade Adegoke ya kasance shi kadai ne a cikin motar sa yana tuki yayin
da wannan abu ya faru.
Mai Martaba yayi karo da wata gingimari ne a Ranar
Larabar nan cikin dare, kimanin karfe 10:00. Ko da mutane suka kawo dauki, an
samu Sarkin ya cika. Wadanda suka ga abin, sun ce Sarkin ya aukawa wannan
katuwar gingimari ne yayin da yake kokarin kaucewa wata motar.
Kwanan nan ne dai aka kai karar Sarkin Kotu, inda ake
kukan yana yi wa Talakawa kwacen gonaki da gidaje. An zargi Sarkin da karya
kasuwancin Jama’a da dama ta hanyar turo ‘yan ta’adda su karya mutum.
A watan Jiya ne kuma Gwamnatin Jihar Edo
karkashin Tsohon
Gwamna
Adams Oshiomole ta tsige wani daga cikin masu Sarautar Kasar, An tunbuke Sarki Anselm
Eidenojie. Mai Girma Anselm Eidenojie shi yake rike da Kasar Uromi da ke Yankin
Arewacin Esan na Jihar Edo. Ana zargin mai martaba da yi wa wata mata shegen duka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment