Bikin
Kirismeti: Karuwai sun koka da rashin kasuwa
– Mata masu zaman kan su, sun koka da Bikin Kirismetin bana
– AANU Adegun na NAIJ.com ya zagaya wajen irin wadannan
mata a Legas
– Sun
koka da yadda abubuwa suka tabarbare
Kamar dai yadda aka san
lokutan Biki, musamman irin na Kiresmeti, lokaci ne na cinikayya wajen ‘Yan
kasuwa. Sai dai bana masu zaman kan su sun koka da rashin ciniki, ba kamar da
ba. Adegun na NAIJ.com ya kawo rahoto.
Abin mamaki; mata masu zaman
kan su a Birnin Legas sun ce fa bana abin ba kasuwa. NAIJ.com ta zagaya wani
Babban Gida na irin wannan mata a Unguwar Ikotun ta Legas a Ranar kashegarin
Kiresmeti, sai dai bana abin sam ba kasuwa.
A baya dai a kan saka
wake-wake da kayan kyale-kyale, da ma Matan suna sheke ayar su, bana kuwa
lamari ya sauya. Gurin sai ka ce ba shi ba. Wata daga cikin masu zaman kan tan
tace da Dan Jaridan na mu cewa: ‘Buhari ya gama da mu…’ Matan dai sun koka da
rashin kudi a Kasar. Wata ma dai cewa tayi ba za ta yafewa Buhari ba…
Su kuwa Mutanen Maiduguri
tsalle suke yi, suna murna, inda aka ci galaba kan ‘Yan Kungiyar Boko Haram.
Gwamnan yace yanzu ya san ana Kirismeti tun da ya hau mulki.
No comments:
Post a Comment