– Shugaban Kungiyar MURIC ta
Musulmai ya tsallake rijiya da baya-da baya
– Farfesa Akintola ya bayyana cewa
wasu na nema su ga bayan sa
– Sai
dai ba wannan ba ne karo na farko ba
Darektan Kungiyar nan ta
MURIC ta Musulmai ya bayyana cewa wasu mutane sun yi yunkurin ganin bayan sa.
Farfesa Akintola yace wasu mutane ne suka bi sa har gida a Ranar Lahadin nan da
ta wuce.
An dai san Ishaq Akintola da
Kungiyar MURIC da tsoma baki cikin lamarin harkar Kasa, musamman wanda zai
shafi Musulmai. Farfesa Akintola yace wasu mutane hudu suka dura gidan sa da
sunan suna neman sa.
Malam Yakeen Williams da
Shefiu Ayorinde suka rubuta jawabi a madadin Darektan Kungiyar ta MURIC. Suka
bayyana duka abin da ya wakana. An yada wannan jawabi a kafafen yada labarai na
zamani. Ba dai yau aka fara kai wa Farfesan hari ba, ko shekaru uku da suka
wuce, an samu irin wannan.
Mutane hudu ne dai suka tasan
ma Gidan Farfesa Akintola a Ranar Lahadin nan, suna cikin Katuwar motar Toyota.
Ko da suka isa sai suka ce suna neman Mai-Gidan ne domin su gayyace sa wani
taro, da aka nemi su kira lambar sa idan da gaske ne, duk sai suka gagara. Ana
dai zargin ana nema a sace ko ma kashe Farfesan ne. Kungiyar ta kira Jama’a su
bi a hankali da kuma yi masa addu'a.
Muhammad Malumfashi ya kawo wannan rahoto a Shafin labarai na NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment