– Shugaba Buhari zai fuskanci babban barazana idan ya nemi zarcewa zaben mai zuwa
– Jam’iyyar APC mai mulki ta shiga cikin wani hali
– Akwai yiwuwar a kafa sabuwar Jam’iyya a Kasar
2019: Shugaba Buhari na cikin matsala
Da
alamu ana shirin kafa wata sabuwar Jam’iyyar gangami a Kasar, hakan dai ba
karamin kalubale ne zai zama ga Shugaba Buhari idan har yana da shirin tazarce
a zabe mai zuwa. Yanzu haka Jam’iyyar APC tana cikin wani hali.
Tun
farko dai Jam’iyyar ta samu matsala wajen zaben Shugabannin Majalisa, Shugaban
Kasa yayi tsit har sai da abubuwa suka rincabe. An samu rikici tsakanin Bola
Ahmed Tinubu da kuma Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki. Hakan ya kawo
matsala tsakanin Majalisa da Shugaba Buhari.
Har
wa yau ana ganin akwai wasu da ke kokarin katange Shugaba Buhari da Jama’an sa,
musamman wadanda suka yi masu yakin neman zabe irin su Asiwaju Bola Tinubu. Ta
wani gefen kuma wasu na kokarin hada fada tsakanin Shugaba Buhari da shi Bola
Tinubu.
Yanzu
haka dai Manyan ‘Yan Siyasar Kasar irin su Bola Tinubu da wasu jiga-jigai na
kokarin hada-kai su kafa sabuwar Jam’iyya. Ko da yake Tsohon Gwamnan ya musanya
wannan magana. Amma ko ya abin yake, Siyasar Shugaba Buhari na cikin matsala.
[NAIJ Hausa]
[NAIJ Hausa]
Babu gudu babu Jada baya Buhari in sha Allah muna tare dashi, duk wadanda aka lissafo suna kokarin barin Jamiyyar APC to daka binchika saikaga suna chikin wadanda suka Karya wannan kasar tamu yanzu muka sunkasa samun yadda suke so amma mujezuwa idan suna tunin Talakkawa zasu karbesu to lokachi zainuna
ReplyDelete