Tuesday, December 6, 2016

Za a Hukunta El-Zakzaky-Gwamnatin Kaduna



– Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana ‘Yan Kungiyar IMN a matsayin ‘yan tawaye


– Gwamnati tace za ta hukunta Shugaban Kungiyar Ibrahim El-Zakzaky


– Za a kama El-Zakzaky da laifin mabiyan sa

 


Ta tabbata cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana Kungiyar IMN a matsayin ‘yan tawaye. Wannan yana cikin bayanin da Gwamnatin Jihar ta fitar da shi bayan bincike da aka gudanar na dogon lokaci. 

Takardar da aka fitar jiya ta bayyana cewa ‘Yan Kungiyar IMN din ‘yan tawaye ne masu tada zaune-tsaye don haka dole a dauki mataki game da su. Haka kuma takardar ta nuna cewa dole a Hukunta Ibrahim El-Zakzaky.

Takardar da Gwamnatin Tarayya ta fitar ya nuna cewa ‘Yan Kungiyar IMN din suna bin El-Zakzaky dari-bisa-dari, hakan ta sa ya kamata a kama sa da duk laifin da suka aikata. A rikicin Shi’ar da Soji da ya faru a bara, an hallaka ‘yan shi’a fiye da 300 a Garin. Gwamnatin Jihar tace za ta bar Gwamnatin Tarayya ta Hukunta Sojojin da ke da laifi.

Shugaban Kungiyar ta IMN, Ibrahim Yakub El-Zakzaky yana can a daure, kwanan ne dai wani Babban Kotu ya bada izinin a sake sa da gaggawa.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...