– Babban Dan wasan Najeriya Austin
Jay Jay Okocha ya bayyana dalilin da ya say a ajiye kwallo yana matashi
– Jay Jay Okocha yace rashin taka
leda da kyau ya sa ya bar kwallo
– Babban dan wasan ya bugawa su
Bolton Wanderers daga shekarar 2002 har 2006
Babban
dan wasan Kasar nan kuma tsohon Kyaftin ya bayyana babban dalilin da ya sa ya
ajiye kwallo da wuri. Tsohon mai rike da kambun Super Eagles yace rashin buga
wasanni a kai-a kai ya sa ya ajiye kwallon.
Dan
wasan Duniyan Okocha wanda ake yi wa lakabi da Jay Jay ya ajiye kwallon kafa ne
a shekarar 2008. Wannan abu ya ba kowa mamaki, domin kuwa babu wanda yayi
tsammanin haka. A wancan lokaci Okocha yana da shekaru 34 ne a duniya.
Okocha
yace bai ga amfanin ya horu tun daga Litinin zuwa Jumu’a ba, sai kuma ya buga
wasa na minti 20 a cikin fili. Sannan kuma ya kara dawowa aiki washegari
Lahadi. Okocha yace shi mutum ne mai son takara da bugawa da sauran Jama’a.
Okocha
ya ajiyewa Najeriya kwallo ne a 2006. Kwanaki da aka tambayi tsohon Kocin
Ingila, Sam Allardyce ko wani Kyaftin ne ba zai manta da shi ba, Kocin ya bada
amsa da Okocha. “Idan dai kana neman Kyaftin a cikin fili da waje sai Okocha”,
Inji Allardyce. “Yana jin yaruka dabam-dabam har hudu, ya iya turanci sosai, ya
taimkawa ‘yan Kasar da ba su jin turanci…’ Inji Allardyce.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment