– Jama’a
sun komawa naman kare a Jihar Ekiti
– Duk inda ka je kurum da naman kare ake dagargajewa
– Ana
sayar da karnuka 'yan wata uku N500
Yanzu haka Karnuka sun fara
bacewa a Jihar Ekiti, domin kuwa duk inda ka shiga cin abinci sai dai ka ga
naman kare a cikin miya. Mutanen Jihar Ekiti dai sun komawa naman karnuka.
Hukumar Dillacin labarai na Kasa ta bada wannan labari.
A Garuruwa irin su
Ise-Ekiti, Ado-Ekiti, Ikere-Ekiti da sauran su naman Karen ya zama wani kayan
Gabas, ko ina rububin kare ake yi. A gidaje da wuraren cin abinci ma da Gidan
ruwa, ko ina kare kurum ake babbakawa ba kama hannun yaro.
Yanzu haka har farfesun kare
ake yi a wasu wuraren. Abin dai har ta
kai babu karnuka a kan titi, don kuwa tuni sun shige tukunya. A na sayar da
jariran karnuka a kan N500, manya kuma su kan kai har N15000; ain dai, iya
kudin ka, iya shagalin ka.
A watan Agusta Gwamna Fayose
na Jihar ya sa hannu kan wata doka da ta haramta kiwon shanu da sauran dabbobin
noma a Jihar, Dokar tace duk wanda aka kama ya saba doka, za a daure sa na
rabin shekaru kuma babu damar karbar tara. Dokar ta haramta kiwo daga karfe 6
na yamma har zuwa 7 na safe. Sai dai masana sun ce naman kare yana da illa
kwarai a jikin Dan Adam.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment