– ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan sun nemi Sakataren Gwamnatin Shugaba Buhari ya sauka daga matsayin sa
– Wani bincike da Majalisar tayi, ya nuna cewa Babachir David ba shi da gaskiya
– Sakataren Gwamnatin yana cikin wadanda suka yi gaba da kudin ‘Yan Gudun Hijira da ke Arewa maso Gabas
A
zaman ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan jiya, sun amince cewa lallai Sakataren Gwamnatin na
Tarayya ya sauka daga mukamin sa. Majalisar Dattawan ta bayyana cewa ta gano
Babachir David Lawal ya mikawa kan sa wasu Kwangila domin ‘Yan gudun Hijira na
Yankin.
Wani bincike da Sanata Shehu Sani yayi ya nuna cewa
Kamfanin su Babachir sun samu kwangilar Miliyoyi da aka tsulawa kudi a Yankin
da rikicin Boko Haram ya shafa. Wani Kamfanin su Babachir aka ba kwangilar aske
ciyayi har na sama da Miliyan 200 a Jihar Yobe.
Sanata Melaye yace sai dai Sakataren yayi wuf ya cire
sunan sa daga cikin masu mallakar Kamfanin. Amma Majalisar tace ta bincika ta
gano cewa lallai har yanzu Babachir din yana da hannu a Kamfanin.
An nemi Babachir ya sauka daga matsayin, domin a bincike
sa, kuma a hukunta sa. Sakataren Gwamnatin dai yace ana kokarin bata masa suna
ne kurum.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan a NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment