Tuesday, December 13, 2016

Shin An sauke Shugabannin Hafsun Soji ne?



Ana ta samun rade-radin cewa Shugaban Kasa ya sauke Hafsun Sojin Kasar

 


Shugaban Kasar yace karya ce kurum ake ta yadawa

 


Sai dai kuma Shugaban Hafsun Sojojin Kasar zai ajiye aiki mako mai zuwa

 

 


Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina yace maganar cewa Shugaba Buhari ya sauke Hafsun Sojin Kasar ba gaskiya bane. Femi Adesina yace an kara gishiri a cikin asalin yadda lamarin yake. 

Femi Adesina wanda shine ke ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara game da harkokin yada labarai, yace a maimakon Jaridar su shiga yada labarai na karya, da sun bincika, sun ji yadda maganar ta ke.

An rahoto cewa Shugaba Buhari ya sauke Janar Olanishakin wanda shine Shugaban Hafsun Sojojin Najeriya da kuma Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas watau Hafsun Sojin ruwa. Sai dai Shugaban Kasan ya bayyana yadda abin yake. 

Femi Adesina ya ce shekarun Janar Olanishakin na aiki sun cika, don haka zai ajiye aiki. Shi kuwa Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas har yanzu da sauran shekarun aiki a gaban sa, don haka yana nan. Amma Janar Olanishakin zai yi ritaya mako mai zuwa, kuma har yanzu ba a fadi wanda zai maye gurbin sa ba.

[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...