– Diyar Tsohon Shugaban Kasar Mozambique ta bakunci lahira Ranar Laraba
– ‘Yan bindiga sun harbe Diyar Tsohon Shugaba Armando Guebuza
– An harbe ‘Yar Ta’alikar a Garin Maputo
A Kasar Mozambique dai Diyar Tsohon Shugaban
Kasar aka kashe. ‘Yan Bindinga sun harbe Misis Guebuza wanda hakan yayi
sanadiyar ajalin ta. Diyar Shugaban tana da shekaru 36 a Duniya. Wannan abu ya
faru ne kwanan biyu da suka wuce a Babban Birnin Maputo.
Diyar Tsohon Shugaban ta sha harbi ratata a jikin
ta, kafin a kai Asibiti, ta cika. Jaridar Kasar tace yanzu haka an kama Mijin
Diyar Tsohon Shugaban Kasar. ‘Yan Sanda sun yi ram da Zofina Mujane.
Mijin na ta Mujane yayi aiki da Kamfanin Sigari
ta Turawa. Misis Guebuza kuma Babbar Ma’aikaciya ce kuna Hamshakiya a Kamfunan
sadarwa, tana kuma cikin harkar kasuwancin gidan na su. Shekaru biyu da suka
wuce ne dai tayi aure da Zofina Mujane inda mutane kusan 2000 suka halarta.
Misis Guebuza dai tana cikin manyan mata da ake
ji da su a Duniya. Jaridar Forbes ta saka ta cikin manyan matan Duniya. A jerin
hamshakan ‘Yan Mata na Nahiyar Afrika, ita ce ta 7.
A Kasar Ghana kuwa, Diyar Shugaban Kasar Ghana
John Mahama, ta rubuta wata wasika mai ban tausayi da saka kwarin gwiwa zuwa ga
Mahaifin ta. Mahama dai ya sha kashi ne a zaben da aka yi a Kasar.
A gida Najeriya kuwa, Diyar Shugaba Buhari,
Zahara Buhari ta auri Ahmed Muhammad Indimi. An daure auren ne a Abuja, inda
Manyan mutane na Kasar nan suka samu halarta.
Muhammad Malumfashi,
No comments:
Post a Comment