– Wani Tsohon mai fiye da shekaru 100 a Duniya zai yi zaman kaso
– Za a daure wannan tsoho na shekaru 13 a Gidan maza
– An kama wannan tsoho da laifuffuka sama da 21
An kama wani Tsoho gota-gotai da shi da lafin daurin na
shekara da shekaru. Yanzu haka dai za a daure wannan tsoho mai sama da shekaru
Da 101 na shekaru 13 a Gidan Yari a
Kasar Birtaniya.
Duk Kasar Birtaniya da wuya a samu Tsohon da zai shiga
Gidan Maza mai sa’ar wannan mutumi da ya ba shekaru 100 baya. Kotun da ke
Birmingham ta kama wannna tsoho da laifuffuka sama da 21. Sunan wannan mutumi
Raplph Clarks.
An kama wannan mutumi da laifin yin lalata da yara kanana
masu shekaru 5 zuwa 13 a wancan lokaci. Wadanda abin ya auku gare su, sun tsufa
yanzu, don sun kere shekaru 40 a yanzu. Sai dai Tsohon yace karya ake yi masa
kurum.
Wani yaro dai ya bayyana cewa tabbas Tsohon yayi lalata
da shi loakcin baya. Yaron ya bayyanawa Kotu ne hakikanin yadda abin yake.
Tsohon ya kasance yana tuka Gingimari.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment