– Shugaban Bangaren PDP, Ali Modu Sheriff ya aurar da diyar sa a karshen wannan makon
– Manyan mutane da dama sun halarci wannan taron
– Da alamu kuma auren Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra ya matso kusa
Diyar Tsohon Gwamnan za ta auri Dogarin Buratai
Tsohon Gwamnan Jihar Borno,
kuma Shugaban bangaren PDP, Alhaji Ali Modu Sheriff ya aurar da diyar sa wannan
makon da ya wuce. Diyar Tsohon Gwamnan, Halima ta auri wani Soja ne mai suna
Ronnie Kabo.
Ronnie Kabo dai matashi ne,
da bai wuce shekara talatin ba, kuma Kyaftin din Soji, ya shiga daga ciki tare
da tsaleliyar Amaryar sa Halima Ali Sheriff. Manyan ‘Yan Siyasan Najeriya sun
halarci wannan taro.
Tsohon Mataimakin Shugaban
Kasa, Atiku Abubakar ya halarci wannan taro. Haka kuma Baba Shehuri; wanda yake
Minista a yanzu. Tsofaffin Gwamnoni irin su Sule Lamido da Ibrahim Shekarau, da
kuma Babangida Aliyu duk sun samu zuwa daurin auren.
Taron
Jama’a sun halarci Bikin Auren Diyar Ali Modu Sheriff; yaushe kuma za a daura
auren Zahra Buhari?
Muna kuma samun
kishin-kishin din cewa an sa Ranar auren Zahra Buhari; za a daura auren diyar
Shugaban Kasar ne a Ranar 16 ga wannan wata, a Babban Masallacin Abuja, bayan
Sallar Jumu’a. Zahra Buhari za ta auri Ahmed
Muhammad Indimi.
No comments:
Post a Comment