– Dubunnan Samari ke dauke da kwayar cutar Kanjamau a Jihar Benue
– Bincike ya nuna cewa matasa sama da 14,000 ke tare da wannan mugun cuta
– Shugaban masu Kanjamu ya bayyana haka
Shugaban Kungiyar masu cutar
Kanjamau ya bayyana cewa samari da ‘yan mata fiye da 14,000 ke fama da cuta
Kanjamau-watau HIV/AIDS a Jihar Benue. Shugaban masu Kanjamau din ya bayyana
haka ne wannan makon a Garin Makurdi.
Shugaban masu Cutar sida
yayi wannan jawabi ne a Ranar Kanjamau ta Duniya wanda aka yi kwanan nan. Yake
cewa abin yayi yawa kwarai, Shugaban yake cewa ana shirin samar da magunguna ga
‘Ya ‘yan Kungiyar domin kawo saukin cutar.
Shugaban Kungiyar, Fabian
Tor yace idan aka samu magani, shi zai kawo sauki ga masu cutar. Darektan
Kungiyar UNAIDS na Cutar Kanjamau a Kasar, Dr. Camara Bilali yace Jihar Benue
na cikin Jihohin da suka fi kowa fama da cutar Kanjamau.
Kungiyar UNAIDS ta Majalisar
Dinkin Duniya mai kula da Kanjamau tace ya zama aikin mu gaba daya mu tashi
tsaye wajen yakar wannan cuta. Kwanan ne a aka gano cewa mutane kusan 10,000 ke
dauke da kwayar cutar ta Kanjamau a Jihar Legas.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment