– Ana shirin tunbuke Shugaban Kasar Gambia babu
girma, ba arziki
– Kungiyar ECOWAS tace ta tanadi
Sojojin da za su kutsa Gambia
– Sojojin Najeriya ne dai kan gaba
Kwanakin baya ne Shugaban Kasar
Gambia ya sanar a Gidan Talabiji cewa ba abin da zai sa ya sauka daga
Shugabancin Kasar. Karshen makon jiya ne Shugaba Buhari
da wasu Shugabannin Afrika su ka kai ziyara Kasar domin ganin Shugaba Jammeh ya amince da
sakamakon zaben da ya sha kashi.
Sai dai Shugaba Jammeh yace ziyarar da su
Buhari suka kai bai canza komai ba. Yace babu dalilin da zai sa ya sauka daga
mulkin Kasar. Don haka Kungiyar ECOWAS na shirya bataliya guda na Sojoji da za su
kutsa Kasar su ga cewa an sauke Shugaba Jammeh da karfin tsiya.
Premium Times tace Marcel de
Souza na Kungiyar ECOWAS ke cewa idan har wa’adin Shugaba Jammeh ya cika, bai
sauka ba, za a bi ta karfi da yaji a tunbuke sa ba girma ba arziki. Sojojin
Najeriya ne dai kan gaba cikin Rundunar da aka tanada masu shiga Kasar. An dai
san Sojin Najeriya da kokari a Nahiyar.
Shugaban Kasar Jammeh, yayi
amai ya lashe game da sakamakon zaben. Shugaba Jammeh ya fi shekara 20 yana
mulkin
Kasar Gambia.
No comments:
Post a Comment