Tuesday, December 27, 2016

Ta auri dan wasan kwallon kafa


– Wata Budurwa mai suna Saudah ta auri dan wasan Najeriya


Saudah ta auri Musa Yahata, wanda ya bugawa Najeriya tamola


An yi auren ne a Garin Kaduna




A wannan makon ne dai aka daura auren Musa Yahaya da Amaryar sa Hajiya Saudah. Musa Yahaya Dan wasan Kwallon Kafa ne wanda ya bugawa Najeriya a mataki na samartaka dabam-dabam.

Musa ya bugawa Najeriya Gasar ‘Yan wasan Kasa da shekaru 17 watau U- 17 da kuma U-20. Sannan Musa ya wakilci Kasar nan a Gasar Olympics na masu shekaru kasa da 23. Dan wasa Musa Yahaya dai yanzu haka yana taka leda ne a kasar Portugal ta Turai.

An dai daura wannan aure ne a Kaduna. Manyan Taurarin ‘Yan wasa irin su Lukman Zakari, Sulaiman watau ‘Daddy’, Alfa Abdullahi da Kocin Dan wasan Manu Garba da sauran Jama’a suka halarci wannan Biki.

Ko da yake dai ana cewa Amaryar Saudah, ‘Yar wasan kwaikwayo ce, da alamu ta musanya wannan magana. Tana dai sha’awar kwallon kafa kamar yadda ta bayyana.

Allah ya ba su zaman lafiya…



Ango, a bakin aiki...

[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...