Thursday, December 8, 2016

Majalisa na nema a kafa Kotun Ikiliziya


Majalisa ta kawo kudirin kafa Kotun Kirista a Kasa




– Wani Dan Majalisa ya kawo kudirin kafa Kotun Kirista a Najeriya

 


Yanzu har wannan kudiri ya tsallake mataki na biyu

 


Hon. Gyang Dung na mazabar Plateau ya kawo wannan kudiri


 

Wani Dan Majalisa Wakilai ta Tarayya mai suna Hon. Gyang Dung daga Jihar Plateau ya kawo wani kudiri zuwa Majalisar Kasar inda yake nema a kafa Kotun Kirista a fadin Kasar nan. Watau dai wannan zai yi daidai da kamar Kotun Shari’ah na Musulunci.  

Yanzu dai haka wannan kudiri na kafa Kotun Ikilisiya ya samu tsallake mataki na biyu a Fadar Majalisar. Hon. Gyang Dung na PDP da ke wakiltar mazabar Plateau ne ya gabatar da kudirin tare da wasu ‘Yan Majalisa 8. 

Dan Majalisan yace idan har an kafa wannan Kotu, za ta zama tana aiki musamman ga abubuwan da suka shafi Addinin Kirista. Hon. Dung ya bayyanawa manema labarai cewa Kotun ba za tayi aiki a kan wanda bai yadda da Ikiliziya da Addinin Kirista ba. 

Sai anyi wa dokar Kasar nan garambawul dai kafin a shigar da wannan kudiri cikin dokar tsarin mulkin Kasa.

[NAIJ Hausa]


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...