– ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan za su fara binciken kudin mai da suka bace a Gwamnatin Shugaba Buhari
– Ana zargin NNPC ta sha kwana da wasu Dala Biliyan 6.9
– An dai saba sace kudin man Kasar ta asusun NNPC
A
zaman ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan sun amince cewa lallai za a binciki wasu kudi da suka
bata a Gwamnatin Shugaba Buhari. Majalisar tace bai kamata wasu kudi su rika
bacewa daga asusun Gwamnatin ba yayin da ake fama da rashin kudi a Kasar.
Sanata Dino Melaye ne ya kawo kudirin cewa ya kamata a
duba wannan batu, Sanata Ali Ndume; Shugaban masu rinjaye a Majalisar kuwa ya
mara masa baya. Sanatan yace kudi kusan
Dalan Biliyan 7 sun yi kafa daga NNPC da kuma NPDC.
Majalisar za ta binciki Shugaba Buhari da kuma Ma’aikatar
mai; Dr. Ibe Kachikwu da kuma Shugaban Kamfanin mai na Kasar watau NNPC;
Maikanti Baru. Majalisar Dattawar kuma za ta binciki Gwamnan Babban Bankin
Kasar; Godwin Emefiele.
Shugaban Majalisar Dattawar, Abubakar Bukola Saraki yace
wasu na kokarin ganin yaki da cin hanci da rashawan da wannan Gwamnati ta ke yi
bai kai ga ci ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment