Wednesday, December 14, 2016

Boko Haram: Yaki ya kusa karewa Inji Buratai

Janar TY Buratai yace so samu kowane Soja ya koma Bariki a shekara mai zuwa

 


Hafsun Sojin Kasar yace an kusa kawo karshen Boko Haram

 


Janar Buratai yayi alkawarin sauya Sojojin da ke filin daga a kan kari




Hafsun Sojin Kasa na Najeriya, Laftana-Janar Tukur Buratai yace zuwa shekarar 2017 Sojojin Kasar nan da ke fada da ‘Yan Boko Haram za su koma bariki. Janar Buratai yace yakin ya kusa zuwa karshe. 

Janar Buratai yace idan so samu ne, zuwa badi kowane Soja ya koma gida. Shugaban Sojojin Kasan yayi wannan magana ne lokacin da ya ziyarci Rundunar Sojin Kasar a Ranar Litinin. Kwanan nan ne dai Bam suka yi ta tashi a Arewa-maso-Gabas.

Buratai yace dole zuwa karshen Disamban nan su gama lallasa ‘Yan Boko Haram da suka rage a Kasar. Janar din yace yayi alkawarin Soji da yawa za su koma gidajen su shekara mai zuwa. Buratai yace za a riga canza Sojojin da ke bakin daga bayan watanni 6, kuma yayi alkawarin sakin kudin su a kai-a kai. 

Jiya ne kuma Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Femi Adesina yace maganar cewa Shugaba Buhari ya sauke wasu Hafsun Sojin Kasar ba gaskiya bane. 


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...