– An kashe wani Saurayi mai shekaru 22 saboda Biredi
– Wani Jami’in tsaron ne soka masa
wuka
– Wannan
abu ya faru ne a Jihar Bayelsa
Wani Sabon kurtum Soja ya
kashe wani Saurayi a Jihar Bayelsa saboda Biredin N50. Wannan abu ya faru ne
dai a farkon wannan makon a Unguwar da ake cewa Ozizebiri da ke Karamar Hukumar
Kudancin Ijaw.
Wani kurtun Soja mai suna
Ayibakare Oguo ya dabawa wannan Saurayi wuka bayan sun yi ‘yar rigima. Sojan ya
yi wa Kanwar Marigayin shegen duka ne saboda Biredin N50. Bayan danuwan ya ga
abin da ya faru, sai yayi kokarin kare kanwar ta sa, daga nan ne fada ya shiga
tsakani.
Kafin ka ce mene dai har Sojan
ya dabawa wannan Saurayi wuka, ya kuwa aika sa Lahira. Wannan abu dai ya kawo
tashin hankali yanzu. Jaridar Punch tace an kona gidaje sama da uku a Yankin.
A Jiya Jumu’a da safe kuma,
Mutanen Garin Zariya sun shiga cikin wani rikici. Jama’a da dama dai sun dauka
fashi aka yi kokarin yi a Unguwar PZ. Inda aka samu takaddama har ta kai wani
Jami’in Mobile ya shiga budawa wuta babu dalili.
No comments:
Post a Comment