Friday, December 16, 2016

Ta Tabbata: Ministar Buhari ta samu aiki a UN

Ministar Buhari ta samu babban matsayi a Majalisar Dinkin Duniya

 


UN ta nada Amina J. Mohammed a matsayin Mataimakiyar Shugaba

 


– Amina J. Mohammed tayi aiki da Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar mai-barin gado

 


Ta tabbata, Majalisar Dinkin Duniya watau UN ta dauke daya daga cikin Ministocin Najeriya. Kamar yadda muka kawo maku labari a baya, Majalisar Dinkin Duniya ta nada Ministar Najeriya mukamin Mataimakiyar Sakatariyar ta. 

Sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya nada wasu matan guda 2 cikin Majalisar. Antonio Gutirres wanda ya zama Shugaban Majalisar na 9 a Tarihi, ya nada Amina J. Mohammed a matsayin Mataimakiyar sa. 

Stephane Dujarric, mai magana da bakin Shugaban Majalisar ya sanar da haka. Sabon Shugaban ya kuma nada wasu matan; Misis Maria Luiza Riberiro Viotti daga Kasar India da kuma Misis Kyung-wha Kang daga Kasar Korea. 

Amina J. Mohammed tana dai cikin Ministocin da suka fi kowa kokari a Gwamnatin Shugaba Buhari. A baya kuma tayi aiki da Ban ki-Moon a Majalisar Dinkin Duniyar. Sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniyan zai fara aiki ne farkon shekara mai zuwa, zai kuma yi shekaru 4. 




[Muhammad Malumfashi, NAIJ Hausa]





No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...