– Gwamnan Jihar Cross River ya bayyana dalilin sa na daukar mashawarta sama da 6, 000
– Gwamnan yace yana kokarin rage rashin aikin yi ne a Jihar
– Ben Ayade ya raba kudi ga Kungiyoyin Addini na Jihar Cross River
Gwamnan Jihar Cross-River, Ben Ayade ya bayyana dalilin da ya sa yake neman
daukan Ma’aikata 50, 000 a shekara mai zuwa. An rahoto kuma Gwamnan yana kokari
nada masu basa shawara guda 6, 000 a Jihar.
Gwamnan yace zai yi haka ne domin Gwamnati ta rika yi da kowa. Gwamna Ayade
yace idan har aka yi haka, kowane Gida zai samu jin danshin Gwamnatin Jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Filin wasa na U.J Esuene da ke Jihar.
Gwamnan ya samu nasara ne dai a Kotun Kolin Kasar bayan an kalubalance
nasarar da ya samu a zaben a Kotu. Kwanaki PDP ta
nemi Kotun Koli ta tsige Gwamnan na Jihar Cross River daga kujerar sa, duk da cewa kuwa
Gwamnan dan Jam’iyyar PDP din ne. PDP tace Gwamnan yayi karyar shekarun sa lokacin neman zabe.
Gwamnan ya kuma raba kyautar Naira Miliyan 30 ga Kungiyar Musulmai da kuma
Naira Miliyan 50 ga Kungiyar Kirista ta CAN. Gwamnan yace sai ya tabbatar babu
wanda ya kwana da yunwa a Jihar don haka zai dauki wadannan uban ma’aikata
badi.
Karanta shafin NAIJ Hausa domin samun cikakkun labarai
No comments:
Post a Comment