– Ashe dama kare na cin mutum?
– Wani kare ya cinye wani jinjiri da aka jefar a bola
– Wannan abin al’ajabi ya faru ne a Jihar Bauchi
Wani
abin ban mamaki matuka ya faru a Garin Bauchi a cikin kwanan nan. Wani kare ne
dai ya cinye wani jinjiri. Ashe ko dama kare na cin mutum?
Jaridar
Vanguard ta rahoto cewa an samu wani kare yana cin wani jinjiri da aka jefar a
bola a Garin Gwallameji na Jihar Bauchi. Wannan abu ya faru ne a wajen Makarantar
Polytechnic da ke Jihar Bauchi.
Wasu
ne dai suka jefar da jinjiri a bolar da ke wurin. Sai dai aka ga kurum kare ya
sa baki yana cinye wannan jariri. Mutane da dama sun ga wannan abu mai ban
al’ajabi.
Wani mai suna Isiah yace ya dawo Coci kenan ya ga jama’a an taru, ko
da ya samu zuwa inda aka taru sai ya ga abin da yake faruwa. Yace abin duk
kyama, ya iske kare yana cin jaririn da aka jefar.
Mai
Garin Gwallameji ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ba ya wajen sa’ilin da abin ya
faru amma ya samu labarin abin da ya auku. Ba dai yawa bane farau da aka samu
an jefar da jariri a wannan Yankin ko ma Kasar ta mu.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment