– Tsohon Gwamnan Jihar Gombe,
Danjuma Goje na shirin maido wasu makudan kudi ga Hukumar EFCC
– Gwamnan da Sanata ne a yanzu yana
neman a sasanta da Hukumar EFCC
– Sai dai Hukumar tace fa sai
an yi aman abin da aka ci
Tsohon
Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanata a yanzu, Alhaji Danjuma Goje zai maido akalla
Naira Miliyan 40 daga cikin kudin da ake zargin ya yi awon gaba da su. Sanata
Goje da wasu Mutane hudu suna hannun EFCC bisa zargin sama da wasu kudi har
Naira Biliayan 25.
Cikin
wadanda ake zargi akwai wanda ya kasance mai kai abinci Gidan Gwamnati a
lokacin Goje yana Gwamna; Alhaji Sabo Muhammad Tumu. Akwai Alhaji Aliyu
El-Nafaty da wani Dan Kasuwa; M. Dokoto.
Ana
dai zargin Tsohon Gwamnan da karkatar da wasu kudin kwangila da na ‘Yan
Majalisu. An dai dauki shekaru fiye da biyar ana shari’ar. Jaridar The Nation
tace Hukumar EFCC na neman Tsohon Gwamnan yayi aman kudin, sai dais hi yana
rokon alfarma, ayi ta-ta kare a wajen Kotu.
Kwanan
nan kuma ana ta samun wasu bayanai masu cin-karo da juna a game da Majalisar
Dattawar da kuma Ibrahim Magu na EFCC. Daya daga cikin Sanatocin Kasar yace ba
gaskiya bane ace Majalisar ba ta amince da Ibrahim Magu ba a matsayin Shugaban
Hukumar EFCC. Ana dai zargi akwai wasu da ke kokarin ganin bayan Magu na EFCC
din.
No comments:
Post a Comment