– Sunan Abubakar Shekau ya samu shiga cikin Manyan Musulman Duniya
– An kuma saka sunan Shugaba Buhari da Sultan, Abubakar Sa’ad
– Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha cewa ‘Yan Boko Haram din ba musulunci suke yi ba
Wata Jarida ta lissafo sunayen Musulman da suka yi kaurin-suna a Duniya, a ciki har da su Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Sauran wadanda suke cikin jerin sun hada da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Sarkin Musulmi, da irin su Hamshakin Dan Kasuwan nan, Aliko Dangote.
Ko
a shekarar bara an saka sunan Shugaba Buhari a matsayin Musulman da suka yi
fice a Duniya. Jaridar ta kuma bayyana cewa Musulmai sun kusa kai kashi daya
cikin hudu na mutanen Duniya; akwai Musulmai kusan biliyan biyu.
Shugaba
Buhari ne na 17 a jeringiyar sunayen Mutane 500 din da aka jero. Ciki kuma
akwai Sarkin Musulmi; Abubakar Sa’ad III. Akwai kuma Babban dan kasuwan nan
Alhaji Aliko Dangote da ma kuma Babban malamin nan Shehi Ibraheem Saleh.
Sannan
dai an saka sunan Abubakar Shekau a ciki Musulmai 500 da suka yi fice. Sai dai
wasu na ganin bai dace a ambaci Shekau din cikin wannan sahu ba. Boko Haram dai
ta kashe mutane fiye da 30,000 karkashin shugabancin Abubakar Shekau. Ya
kasance yana amfani da kananan yara mata wajen tada bam da sunan Addinin
Musulunci wanda har ISIS sai da ta gargade sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment