Asirin Gwamna Wike ya tonu
– An kama Gwamnan Rivers, Nyesom Wike a wayar tarho yana kokarin murde zabe
– An ji cewa Gwamnan ya biya Ma’aikatan Hukumar zabe kudi domin su yi murdiya
– Gwamnan yace zai kashe Ma’aikatan INEC din idan ba su yi yarda yake so ba
Ku
maido mani kudi na ko in kashe ku… Aka ji Wike yana fadawa Ma'aikatan INEC a tarho
An samu muryar wayar tarho
da Gwamnan Jihar Rivers yayi da Jami’in Hukumar zabe na INEC. An ji Gwamnan da
kan sa yana shan alwashin kashe daya daga cikin Jami’an zaben da aka turo Jihar
daga Plateau.
Sahara Reporters ce dai ta
fito da wannan sako. An ji cewa Gwamnan yayi alkawarin kashe wani Jami’i da ya
gagara. Da alamu Jami’in Hukumar zaben ya ki amincewa da ya saka hannu a
takardun zaben ne. Gwamna Wike yace zai kashe kowane ne.
A cikin wayar an ji Gwamnan
yana fada da Turanci cewa ‘zan tabbatar
na kashe shi… zan ga bayan sa a Jihar nan. Ba matsala.’ Gwamnan yake cewa:
‘Ka kira wannan wanda aka turo daga Plateau, ya gargadi mutanen sa da ke Khana…
duk abin da muka basa… Idan ba haka ba, ba zai bar Jihar nan lafiya ba'
Dama dai Jam’iyyar APC tace
Gwamna Wike yayi tafka magudi a zaben da ya gudana makon da ya gabata.
No comments:
Post a Comment